Gwamnatin Jihar Neja ta sanya dokar hana fita a wasu yankunan ƙaramar hukumar Rafi bayan wani sabon rikicin ƙabilanci da ya yi sanadin mutuwar kimanin mutum 80 tare da lalata dukiyoyi.
Gwamna Umaru Bago ya sanar da matakin ne yayin ziyarar da ya kai yankin Tashar Bako, inda rikicin ya ɓarke tsakanin al’ummar Kamuku da Fulani.
Ta bakin mataimakinsa, Yakubu Garba, gwamnan ya umarci jami’an tsaro da su ƙara tura jami’ai da kayan aiki domin tabbatar da zaman lafiya da kuma hana rikicin ƙara yaɗuwa.
A cewar gwamnatin jihar, rikicin ya samo asali ne daga taƙaddama kan mallakar gonakin noma.
Gwamna Bago ya kuma umarci Sarkin Kagara, Alhaji Ahmad Garba-Gunna, da ya kafa Kwamitin Zaman Lafiya da Sasanci domin sasanta ɓangarorin da abin ya shafa tare da samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Haka kuma, gwamnan ya yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, tare da gargaɗin masu amfani da kafafen sada zumunta da su guji yaɗa rahotannin da ba a tantance ba ko kuma waɗanda za su iya tayar da fitina.
Ya ce al’ummomin Kamuku da Fulani sun daɗe suna rayuwa cikin zaman lafiya, don haka bai kamata rikicin wasu tsirarun mutane ya lalata dangantakarsu ba.
A nasa ɓangaren, Sarkin Kagara ya yaba da matakin gaggawar da gwamnatin jihar da jami’an tsaro suka ɗauka, tare da kira ga hukumomin tsaro da su kamo tare da gurfanar da waɗanda suka haddasa rikicin.
A yayin ziyarar, mataimakin gwamnan ya kai ziyara sansanonin waɗanda rikicin ya raba da muhallansu da ke Makarantar Firamare ta Tegina da kuma Makarantar Firamare ta Gimi.













