ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

ADC Ta Zargi Gwamnatin Tinubu Da Jefa ‘Yan Nijeriya Miliyan 17 Cikin Yunwa

by Sadiq
2 months ago

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gaza magance matsalar yunwa da ke ƙara ƙamari a Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar na Ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce sama da ‘yan Nijeriya miliyan 17 na fama da matsanancin ƙarancin abinci sakamakon gazawar gwamnati wajen magance rashin tsaro, kare manoma da kuma rage tsadar kayan abinci.

ADC ta yi wannan martani ne bayan rahoton Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya bayyana cewa mutane sama da miliyan 17 a jihohi tara da rikici yake shafa a Arewacin Nijeriya na fuskantar matsananciyar yunwa.

ADVERTISEMENT

Rahoton ya kuma nuna cewa sama da mutane miliyan uku a Jihar Borno na cikin halin yunwa, yayin da adadin mutanen da abin ya shafa a jihohin Borno, Adamawa da Yobe ya kai miliyan 6.2.

Jam’iyyar ta ce rahoton ya tabbatar da cewa rashin tsaro, hare-haren da ake kai wa manoma, da raba al’umma da muhallansu ne suka haddasa ƙarancin abinci, ba wai iftila’in sauyin yanayi ba.

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

Har ila yau, ADC ta soki gwamnatin Tinubu kan ci gaba da cewa matsin tattalin arziƙin da ake fuskanta na wucin gadi ne, tana mai cewa hauhawar farashin kayan abinci da kom bayan noma na ci gaba da ƙara jefa rayuwar al’umma cikin yunwa.

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa idan ta samu damar hawan kan mulki, za ta bai wa harkar samar da abinci muhimmanci ta hanyar tallafa wa manoma, bunƙasa noma, da kuma samar da ingantattun wuraren adana amfanin gona domin rage asara da daidaita farashin kayan abinci.

A ƙarshe, ADC ta yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar yunwa da rashin tsaro da ke addabar ƙasar.

MASU ALAKA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
Next Post
Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano

Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano

LABARAI MASU NASABA

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.