ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz

by Sadiq
2 months ago

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) sun harba aƙalla makamai masu linzami biyu kan wasu jiragen ruwan kasuwanci da ke ratsawa ta Mashigar Hormuz.

Kafar yaɗa labarai ta Axios, ta ce an kai harin ne a daren ranar Litinin, inda wasu jiragen ruwa biyu suka lalace, sai dai babu rahoton asarar rai.

Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta tabbatar da cewa an kai wa wani jirgin dakon mai hari a kusa da yankin Limah da ke ƙasar Oman.

ADVERTISEMENT

Hukumar ta ce harin ya haddasa gobara a jirgin, amma babu wanda ya mutu.

Rahotanni sun ce ɗaya daga cikin jiragen da aka kai wa hari shi ne Al Rekayyat, wani jirgin dakon gas da kamfanin Nakilat na Qatar ke amfani da shi.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

An ce makamin ya faɗa kusa da sashen injin jirgin, lamarin da ya janyo tashin wuta da hayaƙi.

Jaridar Wall Street Journal ta ce duk da harin, ma’aikatan jirgin sun tsira kuma an kai su waje mai aminci a cikin jirgin.

Lamarin na zuwa ne bayan tattaunawar da Amurka da Iran suka yi a makon da ya gabata ba ta kai ga cimma wata sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya ba, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ake fatan za ta rage tashin hankali tsakanin ɓangarorin.

A ranar Litinin, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Amurka za ta cimma yarjejeniya da Iran ko kuma ta ɗauki wasu matakai idan hakan ya gagara.

Masana sun ce rikicin na ci gaba da jefa fargaba a kasuwannin duniya, musamman kan zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma safarar ɗanyen mai ta Mashigar Hormuz, wadda ke daga cikin manyan hanyoyin jigilar mai a duniya.

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Mutane 80 Sun Rasu Sakamakon Rikicin Ƙabilanci

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Mutane 80 Sun Rasu Sakamakon Rikicin Ƙabilanci

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.