ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano

by Sadiq
2 months ago

Hukumar Kula da Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kano, ta tilasta wa wani Alƙalin Kotu yin ritaya bayan samun sa da laifin karɓar cin hanci.

Haka kuma, ta ɗauki matakan ladabtarwa kan wasu alƙalai da ma’aikatan kotu bisa laifukan rashin ɗa’a.

Matakin ya biyo bayan taron hukumar karo na 90 da aka gudanar a ranar 3 ga watan Yuli, bayan nazarin rahotannin Kwamitin Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a kan ma’aikatan shari’a.

ADVERTISEMENT

A cikin wata sanarwa da kakakin Kotunan Jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya fitar, ya ce an ɗauki matakan ne domin kare mutuncin harkar shari’a da inganta amincewar jama’a da kotuna.

Hukumar ta umarci Alƙali Aliyu Yahaya Muhammad na Kotun Shari’a ta Bebeji da ya yi ritaya nan take bayan bincike ya tabbatar da cewa ya karɓi cin hancin Naira 250,000 yayin gudanar da wata shari’a.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Haka kuma, an umarce shi da ya mayar da kuɗin.

Sai kuma magatakardar kotun, Ibrahim Ahmad Ibrahim, wanda aka dakatar da shi na tsawon watanni huɗu ba tare da albashi ba, bayan ya amsa cewa ya karɓi wani ɓangare na kuɗin cin hancin.

Har ila yau, hukumar ta tilasta wa Muzambilu Ado, muƙaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Kano, yin ritaya saboda kura-kurai da aka gano a takardun karatunsa da kuma yadda aka ɗauke shi aiki.

Haka kuma, an rage wa Alƙali Usman Haruna Usman na Babbar Kotun Shari’a ta Goron Dutse matsayi saboda sakaci da ya sa aka tura kuɗin da aka samu daga sayar da kadarorin da kotu ta ƙwace zuwa asusun wani ma’aikacin kotu.

Alƙali Abdullahi Wayya na Kotun Kasuwa kuwa gargaɗi aka yi masa saboda sakaci wajen sa ido kan bayar da beli, lamarin da ya sa aka saki wanda ake tuhuma ba tare da cikakken tantance takardun belin ba.

Hukumar ta kuma umarci Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta binciki Sufeto Shehu Adamu bisa zargin yaudarar kotu, tare da ba da umarnin binciken wasu ma’aikatan kotu biyu kan rawar da suka taka wajen bayar da takardun belin.

Hakazalika, hukumar ta janye dakatarwar da ta yi wa Alƙali Umar Sunusi Danbaba bayan sake nazarin wasu sabbin takardu.

Ta kuma mayar masa da albashi da sauran haƙƙoƙinsa tare da umartar sa ya koma bakin aiki.

A ƙarshe, Hukumar Kula da Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta na tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkar shari’a, tana mai gargaɗin cewa duk wani ma’aikacin shari’a da aka samu da laifin cin hanci ko rashin ɗa’a zai fuskanci hukuncin da ya dace da shi.

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO
Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana
Labarai

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Next Post
Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.