Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya ce gwamnatin da Peter Obi zai jagoranta za ta dawo da tallafin man fetur, amma ta wata hanya daban.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Talata, yayin da yake magana kan farashin man fetur da kuma zaɓen 2027.
Ya ce gwamnatin NDC za ta zuba jari wajen gina matatun mai na cikin gida domin ƙara yawan man da ake samarwa a Nijeriya da kuma rage farashin fetur ga ’yan ƙasa.
A cewarsa, gwamnati za ta iya gina ƙarin matatun mai domin tabbatar da cewa Nijeriya na samar da isasshen fetur don amfanin cikin gida.
Kwankwaso ya kuma soki matakin Shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man fetur nan take bayan hawansa mulki a shekarar 2023.
Ya ce matakin ya taimaka wajen tashin farashin mai da tsadar rayuwa.
Tsohon gwamnan na Kano, ya ce idan aka zaɓi NDC, za ta ɗauki matakai domin rage farashin man fetur, inda ya bayyana cewa ya kamata ’yan Nijeriya suke sayen mai a farashi mai sauƙi.













