Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta fara biyan haƙƙokin ritaya ga tsofaffin ma’aikatan gwamnati, inda ta riga ta biya kusan Naira biliyan 1.1 ga mutum 175 da suka yi ritaya daga ma’aikatun gwamnati da kuɗaɗensu ke fitowa kai tsaye daga baitulmalin tarayya, tsakanin 1 ga Janairu zuwa 31 ga Agusta, 2026.
Hukumar Kula da Fansho ta Ƙasa (PenCom) ce ta bayyana hakan a wata sanarwa, inda ta ce ana biyan kuɗaɗen ne ƙarƙashin Shirin Garabasar Ritaya na Gwamnatin Tarayya (Exit Benefit Scheme), wanda Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da shi, kuma ya fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026.
A ƙarƙashin shirin, ma’aikatan gwamnatin tarayya da suka yi aiki na aƙalla shekaru 10 za su cancanci samun ƙarin kuɗin ritaya da ya yi daidai da kashi 100 cikin 100 na jimillar albashinsu da alawus-alawus na shekara. Wannan kuɗi ƙari ne kan fansho da sauran kuɗaɗen da ma’aikaci ya tara a Asusun Ajiyar Ritayarsa (RSA).
PenCom ta bayyana cewa kasafin kuɗin shekarar 2026 ya ware Naira biliyan 32.9 domin gudanar da shirin, yayin da Gwamnatin Tarayya ta saki Naira biliyan 12.3 zuwa asusun musamman na shirin da ke Babban Bankin Nijeriya (CBN).
Hukumar ta ce masu ritaya za su miƙa takardun sallama daga aiki da takardun albashi na baya-bayan nan ga kamfanonin kula da fanshonsu (PFA), waɗanda za su tantance bayanansu kafin aika su PenCom domin sahalewa. Bayan amincewa, za a saka kuɗin cikin asusun RSA ɗin mai ritaya, sannan PFA ta tura shi zuwa asusun bankin da yake karɓar albashi.














