ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 22, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Ceto Mutane 23 Da Aka Yi Garkuwa Da Su, Sun Kama Mutum 4 A Sakkwato

by Abubakar Sulaiman
12 hours ago

LABARAI MASU NASABA

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyu, Sun Kwashe Dabbobi A Sokoto

Gwamnatin Zamfara Ta Ƙara Albashin Ma’aikatan Lafiya Da Kashi 95

Dakarun Operation FANSAN YAMMA a Arewa maso Yamma sun ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su tare da kama mutum huɗu da ake zargin mambobin ƙungiyar Lakurawa ne a wasu sumame daban-daban a Jihar Sakkwato. An gudanar da ayyukan ne ranar Lahadi, 20 ga Satumba, 2026, a ƙananan hukumomin Wurno, Sabon Birni, Isa da Illela.

Jami’an sojin sun ce sun mayar da martani kan harin da ’yan ta’addan suka kai Sabon Gari, cikin Ƙaramar Hukumar Wurno, inda suka buɗe wa mazauna garin wuta. Sojojin sun fatattaki maharan, tare da ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su. Wani farar hula da harsashi ya ji wa rauni a yayin harin shi ma an kai shi asibiti domin samun kulawar lafiya.

A wani sumame da aka kai kan hanyar Sabon Birni zuwa Takatsaba, musamman yankin Chabe Biyu, sojojin sun yi kwanton-bauna bisa bayanan sirri kan yunƙurin ’yan ta’addan ratsa yankin. Bayan ganinsu, sojojin sun buɗe musu wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa. Haka kuma, bayan samun kiran neman agaji a hanyar Isa zuwa Kwanar Isa zuwa Shinkafi, sojojin sun fafata da maharan tare da tilasta musu ja da baya, inda binciken da aka gudanar daga bisani ya kai ga ceto mutane 17 da aka yi garkuwa da su.

ADVERTISEMENT

A Ƙaramar Hukumar Illela kuma, sojojin sun kama mutum huɗu da ake zargin mambobin Lakurawa ne bayan samun bayanan sirri cewa suna ƙoƙarin kwashe wasu shanu da ake zargin an sace daga ƙauyen Sarma zuwa Illela. An kuma kwato shanu shida, yayin da ake tsare da waɗanda ake zargin domin ci gaba da bincike. Rundunar ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin cafke sauran waɗanda suka tsere.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    EFCC Ta Kafa Tawagar Binciken Atiku, Malami Da Wasu Kan Batun Wutar Mambilla
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Biya Ƴan Fansho Naira Biliyan 1.1
  • Abubakar Sulaiman
    Zargin Taimakwa Ƴan Bindiga, Mai PoS Ya Shiga Hannu A Katsina
  • Abubakar Sulaiman
    Dole Tinubu Yayi Bayin Dalilin Rashin Halartar UNGA Har Sau 3 – Atiku

MASU ALAKA

Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
Labarai

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyu, Sun Kwashe Dabbobi A Sokoto

September 21, 2026
Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York
Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Ƙara Albashin Ma’aikatan Lafiya Da Kashi 95

September 21, 2026
Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 
Manyan Labarai

Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 

September 21, 2026
Next Post
EFCC Ta Kafa Tawagar Binciken Atiku, Malami Da Wasu Kan Batun Wutar Mambilla

EFCC Ta Kafa Tawagar Binciken Atiku, Malami Da Wasu Kan Batun Wutar Mambilla

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York

An Gudanar Da Tattaunawar Tattalin Arziki Da Kasuwanci Tsakanin Sin Da Amurka A New York

September 21, 2026
Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

Gwamnatin Sin Ta Sha Alwashin Tallafawa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu Da Ake Da Kyakkyawan Fata A Kansu

September 21, 2026
Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

Sin Za Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Manyan Jami’ai Kan Cika Shekaru 5 Da Kaddamar Da Shawarar Raya Ci Gaban Duniya

September 21, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyu, Sun Kwashe Dabbobi A Sokoto

September 21, 2026
Ko Wadanne Gudanmawa Manufar Gaggauta Cinikayyar Waje Ta Sin A Fannin Hajojin Dakile Sauyin Yanayi Ka Iya Samarwa Duniya?

Ko Wadanne Gudanmawa Manufar Gaggauta Cinikayyar Waje Ta Sin A Fannin Hajojin Dakile Sauyin Yanayi Ka Iya Samarwa Duniya?

September 21, 2026
Xi Ya Mayar Da Amsar Wasikar Daliban Jami’o’in Amurka

Xi Ya Mayar Da Amsar Wasikar Daliban Jami’o’in Amurka

September 21, 2026
Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York

Gwamnatin Zamfara Ta Ƙara Albashin Ma’aikatan Lafiya Da Kashi 95

September 21, 2026
Xi Zai Je Ziyarar Aiki A Amurka Daga Ranar 23 Zuwa 25 Ga Watan Satumba

Xi Zai Je Ziyarar Aiki A Amurka Daga Ranar 23 Zuwa 25 Ga Watan Satumba

September 21, 2026
Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 

Saudiyya Ta Bai Wa NAHCON Shekaru Uku Ta Koma Tsarin Aikin Hajji Na Zamani 

September 21, 2026
Sin Ta Yi Nasarar Noma Nau’o’in Tsirrai 14 A Cibiyarta Ta Binciken Sararin Samaniya

Sin Ta Yi Nasarar Noma Nau’o’in Tsirrai 14 A Cibiyarta Ta Binciken Sararin Samaniya

September 21, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.