Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin Huang Ling, ta ce wakilan Sin da na Amurka na gudanar da tattaunawa game da cimma matsaya kan yiwuwar rage harajin ramuwar gayya, wanda ya shafi hajojin sassan biyu na kimanin dalar Amurka biliyan 30.
Huang Ling, wadda ta bayyana hakan a Alhamis din nan yayin taron manema labarai, ta kuma ce tawagogin kasashen biyu game da batun tattalin arziki da cinikayya, na kokarin aiwatar da sahihiyar matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin ganawarsu ta birnin Beijing.
Manufar tattaunawar dai ita ce kokarin cimma matsaya dangane da tsarin rage harajin ramuwar gayya tsakanin sassan biyu nan ba da jimawa ba. (Saminu Alhassan)














