ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Zamfara Ta Jinjina Wa Shugaban NAHCON Kan Nasarar Aikin Hajjin 2026

by Sulaiman
2 months ago
NAHCON

Gwamnatin Jihar Zamfara ta yaba wa Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Alhaji Isma’il Abba Yusuf, bisa nasarar da aka samu wajen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 cikin tsari da nasara.

Wata tawaga daga gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagorancin Manajan Daraktan Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau, Alhaji Kabiru Yahaya Gusau, ta kai masa ziyarar girmamawa a ranar Alhamis, 2 ga Yuli, 2026, a Hajj House da ke Abuja domin taya shi murnar kammala aikin Hajjin bana cikin nasara.

Tawagar, wadda Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal, ya aike, ta haɗa da Daraktan Kuɗi da Kayayyaki, Alhaji Yahuza Mai Haja; Daraktan Fasahar Sadarwa da Bayanai (ICT) na Hukumar Kula da Harajin Cikin Gida ta Jihar Zamfara, Alhaji Bilyaminu Ahmad Muhammed; da kuma Jami’in Haraji, Alhaji Anas Muhammed Gusau.

ADVERTISEMENT

Da yake jawabi a madadin tawagar, Alhaji Kabiru Yahaya Gusau ya isar da saƙon godiya daga Gwamna Dauda Lawal ga Shugaban NAHCON.Ya yabawa Jakada Isma’il Abba Yusuf bisa nagartaccen jagoranci, kyakkyawan tsari da ingantacciyar daidaitawa, waɗanda ya ce sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da gudanar da aikin Hajjin 2026 cikin nasara.

Har ila yau, tawagar ta nuna gamsuwarta da irin hidimomin da aka samar wa alhazan Nijeriya, tare da yaba kyakkyawar alaƙar aiki tsakanin Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) da Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

A nasa jawabin, Jakada Isma’il Abba Yusuf ya gode wa Gwamna Dauda Lawal da Gwamnatin Jihar Zamfara bisa wannan karamci da girmamawa da suka nuna masa.

Ya bayyana cewa nasarar aikin Hajjin 2026 ba ta taƙaitu gare shi kaɗai ba, illa ta samo asali ne daga haɗin gwiwar ma’aikatan NAHCON, Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da sauran masu ruwa da tsaki.

Shugaban ya kuma jaddada aniyar hukumar na ci gaba da inganta ayyukanta da kyautata hidimomin da ake bai wa alhazan Nijeriya.

An kammala ziyarar ne da gudanar da addu’o’in Allah Ya ci gaba da ba Hukumar Alhazai ta Ƙasa nasara a ayyukanta, tare da ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumar da Gwamnatin Jihar Zamfara wajen tafiyar da harkokin aikin Hajji.

NAHCON
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
CAF Ta Gayyaci Ƙasashen Afirka Su Nemi Ɗaukar Nauyin Gasar AFCON Ta 2028, 2032 da 2036

CAF Ta Gayyaci Ƙasashen Afirka Su Nemi Ɗaukar Nauyin Gasar AFCON Ta 2028, 2032 da 2036

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.