An kashe fitaccen mai sharhin siyasa kuma mai amfani da kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu, a gidansa da ke unguwar Gaida, a ƙaramar hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.
Dan Shagamu ya rasu yana da shekaru 54, ya yi ƙaurin suna wajen sharhi kan harkokin siyasa da sauran al’amuran da suka shafi Nijeriya, musamman a kafafen sada zumunta.
An gano gawarsa a gidansa da safiyar ranar Laraba, lamarin da ya jefa iyalansa, abokansa da mabiyansa cikin tashin hankali.
Lamarin ya faru ne bayan ya taɓa yin budiyo inda ya bayyana cewa ana yi wa rayuwarsa barazana, wanda hakan ya sa ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su kawo masa ɗauki.
“Ana Yi Wa Rayuwata Barazana” — Dan Shagamu
Dan Shagamu ya yi amfani da kafafen sada zumunta wajen bayyana damuwarsa kan barazanar da ya ce ana yi masa.
Marigayin ya taɓa bayyana wa ƙarara cewar ana masa barazana, amma a wancan lokacin wasu sun yi zargin cewa lamarin yana da alaƙa da rikicin da yake samu da maƙwabtansa wanda ya zargi wasu da hannu wajen kitsa masa makirci.
Daga cikin bidiyoyin da ya wallafa, ya nemi a shiga cikin lamarinsa kafin a cutar da shi, inda ya jaddada cewar rayuwarsa na cikin hatsari.
Wannan na daga cikin abubuwan da suka sa kisan nasa ya haifar da alamar tambaya, musamman kan ko hukumomin tsaro sun samu bayanan barazanar da yake fuskanta kafin rasuwarsa.
Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu mutane suna bibiyar rayuwarsa, lamarin da ya sa ya riƙa neman taimakon jami’an tsaro.
Wasu kafafen watsa labarai sun bayyana cewsr wata ’yar uwarsa ta bayyana cewa wasu mutane sun jima suna bibiyar rayuwarsa.
Yadda Aka Gano Gawarsa A Gidansa
‘Yan uwansa sun bayyana cewa sun shiga damuwa ne bayan sun kasa samun sa a waya, kafin daga bisani aka gano gawarsa a cikin gidansa da ke unguwar Gaida.
Rahotanni sun ce an same shi kwance cikin jini, lamarin da ya nuna mutane da yawa ne suka yi masa taron dangi suka kashe shi.
Har yanzu babu cikakken bayani kan yadda aka shiga gidan ko ainihin makamin da aka yi amfani da shi wajen kashe shi.
Hakazalika jami’an tsaro ba su ga wayoyinsa guda biyu ba lokacin da aka gano gawarsa
Jama’a da dama ciki har da ’yan siyasa, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da mabiyansa a kafafen sada zumunta sun yi Allah-wadai da kashe shi.
Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Umarnin Kamo Waɗanda Suka Aikata Laifin
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da kisan, tare da umartar jami’an tsaro da su gaggauta gano waɗanda suka aikata laifin.
Gwamnan ya buƙaci hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da cewa duk waɗanda ke da hannu a kisan sun fuskanci hukunci.
Rundunar ’yansanda da sauran hukumomin tsaro sun fara bincike domin gano musabbabin kisan da kuma waɗanda suka shirya ko suka aikata laifin.
’Yansanda Sun Kama Mutane 2 Da Ake Zargi Da Hannu A Kashe Shi
A yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike, rahotanni sun ce Rundunar ’Yansandan Jihar Kano, ta kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan Dan Shagamu.
Ana yi wa waɗanda aka kama tambayoyi yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin gano cikakken abin da ya faru.
Rahotanni sun ce binciken ya haɗa da ƙoƙarin gano yadda aka shirya kashw shi, waɗanda suka shiga gidan da kuma ko akwai wasu mutane da suka taimaka wajen aikata kisan.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ‘yansanda ba su bayyana sunayen mutane da suka kama da waɗanda ake zargin na da hannu a kisan.
Amnesty Ta Buƙaci A Gudanar Da Bincike
Kisan ya kuma jawo hankalin ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama, Amnesty International, wadda ta yi Allah-wadai da lamarin tare da neman hukumomin Nijeriya su gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da adalci.
Ƙungiyar ta nuna damuwa kan barazanar da mutane masu sharhi kan al’amuran siyasa da sauran mutane masu bayyana ra’ayoyinsu ke fuskanta, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen 2027 a Nijeriya.
Tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, shi ma ya yi Allah-wadai da kisan tare da neman a gudanar da bincike mai zurfi domin gano gaskiyar abin da ya faru.
Yayin da ’yansanda suka kama mutane biyu, babban abin da jama’a ke son ji, shi ne dalilin da ya sa aka hallaka shi har lahira.
Kisan Dan Shagamu ya haifar da fargaba da ce-ce-ku-ce kan yadda ake kare masu bayyana ra’ayoyinsu a bainar jama’a, musamman waɗanda ke yin sharhi kan al’amuran siyasa da kuma sukar gwamnati.
A halin yanzu, ana ci gaba da bincike, yayin da iyalan marigayin da mabiyansa ke jiran ƙarin bayani daga wajen jami’an tsaro.













