Hukumar Kwallon Kafa ta Saudiyya ta dage wasanni uku na gasar Saudi Pro League a wannan makon, sakamakon barazanar tsaro da ta danganta da hare-haren mayakan Houthi.
Wasannin da aka dage sun haɗa da na Al Hilal da Al Riyadh, da Al Ittihad da Al Shabab, waɗanda aka mayar zuwa ranar 19 ga Disamba. Haka kuma, an sauya ranar wasan Al Ahli da Al Nassr zuwa 6 ga Maris, 2027.
Sai dai hukumar ta bayyana cewa sauran wasannin mako na tara za su gudana kamar yadda aka tsara.
A ranar Litinin, an samu tsaikon kusan awa guda a wasan da Al Nassr ta buga da Neftchi Fergana ta Uzbekistan a gasar AFC, bayan hukumomin Saudiyya sun sanar da kakkabo wani makami mai linzami da suka ce mayakan Houthi ne suka harba.














