Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Sakkwato ta yi watsi da karar da Sanata Sahabi Ya’u Kaura ya shigar, yana kalubalantar hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau kan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa.
Kotun ta tabbatar da hukuncin babbar kotun, wadda ta umarci jam’iyyar APC da ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani bayan samun korafin Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, wanda ke ikirarin cewa ba a gudanar da zaben fidda gwani bisa ka’ida ba.
Lauyan wanda ake kara na farko, Bello Galadi, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan yanke hukuncin.
Ya ce kotun ta yi watsi da dukkan hujjojin da Sanata Sahabi Ya’u Kaura ya gabatar, saboda rashin gamsassun hujjoji.
Galadi ya ce Kaura ya kalubalanci hurumin Babbar Kotun Tarayya na sauraron karar, amma Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da cewa kotun tana da ikon sauraron shari’ar da kuma yanke hukunci a kanta.
Ya ƙara da cewa kotun ta kuma yi watsi da hujjar cewa an sauya nauyin tabbatar da hujja ba bisa ka’ida ba, inda ta amince da cewa akwai isassun shaidu da ke nuna rashin bin dokoki da ƙa’idojin jam’iyyar APC.
Lauyan Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya bayyana hukuncin a matsayin babbar nasara ga dimokuradiyya da bin doka da oda.
Ya ce hukuncin ya tabbatar da cewa kowa, ba tare da la’akari da matsayinsa ba, yana ƙarƙashin doka.
A baya, Shinkafi ya shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau, yana zargin cewa ba a gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani na APC na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa ba.
Kotun ta yi hukunci a madadinsa, inda ta umarci a gudanar da sabon zaɓen fidda gwani cikin kwanaki 14.
Sai dai Sanata Sahabi Ya’u Kaura ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
Bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, Shinkafi ya buƙaci magoya bayansa a kananan hukumomin Shinkafi, Birnin Magaji, Zurmi da Kaura Namoda da su ci gaba da fafutukar neman wakilcin siyasa na gaskiya da adalci.














