ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙungiyoyi Sama Da 2,000 Sun Sauya Sheƙa Saboda Matsa Musu A Kaduna – Lawali

by Hussein Yero
2 weeks ago

Darakta mai kula da harkokin matasa na Atiku Pulse, Hon. Lawali Isah Gusau, ya ce matsin lamba da ake yi i wa jam’iyyar adawa ta ADC a Kaduna ya sa jam’iyyar ta ƙara samun karɓuwa a jihar.

Lawali ya ce sama da ƙungiyoyi 2,000 ne suka bar jam’iyyar APC mai mulki a Kaduna suka koma ADC.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a Gusau, inda ya zargi gwamnatin Kaduna da takura wa jam’iyyun adawa, musamman ’yan takarar ADC.

ADVERTISEMENT

Ya yi kira ga shugabannin APC da su guji ɗaukar irin wannan mataki, yana mai cewa abin na iya haifar da sakamakon da ba su zata ba.

Lawali ya kawo misalin zaɓen 2023 a Zamfara, inda ya ce duk da ƙalubalen da ADC ta fuskanta, jam’iyyar ta samu nasara a wasu mazaɓu.

LABARAI MASU NASABA

Me Tinubu Zai Yi Wa Arewa Alƙawari A Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓensa A Kaduna?

MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna

Ya ce hakan ya kamata ya zama darasi ga APC a Kaduna.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Arewa da su yi tunani sosai kafin zaɓen 2027, su guji bin son rai ko wasu ’yan siyasa kawai, sannan su zaɓi shugabannin da suke ganin za su yi aiki domin amfanin jama’a.

Lawali ya kuma ce idan ’yan Nijeriya suka zaɓi ADC da ’yan takararta a zaɓen 2027, yana da yaƙinin cewa za a iya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ta’addanci a ƙasar.

Ya bayyana cewa wannan shi ne ra’ayinsa a matsayin Daraktan Harkokin Matasa na Atiku Pulse kuma ɗan siyasa mazaunin Kaduna.

Hussein Yero
+ postsBio
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Hukumar Zaɓe Ta Wayar Da Kan Nakasassu Kan Kaɗa Ƙuri’a A Zamfara
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Hukuncin Gudanar Da Zaɓen Fidda Gwani Na APC A Zamfara Ta Arewa
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    ’Yan Majalisar Da Suka Sauya Sheƙa Za Su Iya Dawowa APC Idan Sun Nemi Afuwa — Kakakin Majalisar Zamfara
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Marafa Ya Yi Alƙawarin Murabus Idan Ya Kasa Magance Tsaro Cikin Shekaru Biyu

MASU ALAKA

Tinubu Ya Ce Ba Zai Iya Raka ‘Yan Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa Kowace Jiha Ba
Siyasa

Me Tinubu Zai Yi Wa Arewa Alƙawari A Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓensa A Kaduna?

October 24, 2026
MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna
Siyasa

MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna

October 24, 2026
Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’
Siyasa

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

October 23, 2026
Next Post
Yankin Musamman Na Hong Kong Ya Ci Gaba Da Rike Kambin Wuri Mafi ’Yancin Hada-Hadar Tattalin Arziki A Duniya

Yankin Musamman Na Hong Kong Ya Ci Gaba Da Rike Kambin Wuri Mafi ’Yancin Hada-Hadar Tattalin Arziki A Duniya

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.