ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ibrahim Aliyu Na Ci Gaba Da Rasa Tasiri A Harkar Fili Da Gidaje A Yankin Abuja

by Shuaibu Shuaibu
2 months ago

Shugaban kamfanin Urban Shelter, Malam Ibrahim Aliyu, wanda watakila shi ne mafi girman kamfani mai haɓaka rukunin gidage a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma ƙasa baki ɗaya.

A kowace mataki, ya yi tasiri a ɓangaren haɓaka gine-gine da ƙawata Babban Birnin Tarayya Abuja. Hanyar kasuwancinsa ma ta yi tasiri a wasu birane a faɗin ƙasar nan.

Wasu daga cikin manyan ayyukan ci gaba da ya fara gudanarwa a Babban Birnin Tarayya Abuja sun haɗa da gina kasuwar Garki Ultra-Modern Market, kasuwar Apo Urban, Guzape Mall, Kubwa Mall, Urban Shelter Sƙuare, Amina Court a Apo, rukunin gidaje na Katampe, rukunin gidaje na Lake Ɓiew Estate a Kado da kuma Mabushi Priɓate Ɓilla.

ADVERTISEMENT

Haka kuma akwai wasu da suka haɗa da Heritage Heights a Asokoro, da rukunin gidaje a Kyami, Life Camp, Lokogoma, Kubwa, Dawaki da Guzape duka a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Sannan nan akwai wasu ƴan kaɗan kamar su Shelter Ɓalley Residences a Ajiwe, rukunin gidaje na Urban Shelter a Ajayi, Urban Shelter Liɓing Oniru duka a Legas.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Malam Aliyu a ko da yaushe yana da alfanu. Yana samun damar haɗuwa da mutane masu riƙe da muƙamai daban-daban. Kuma hakan yana nufin samun damar mallakar filaye da zuba jari, da kuma samun bashi mara iyaka. Amma yana gina ne kawai don matsakaitan masu arziki na sama.

A ƴan shekarun baya, hannun jarinsa a kasuwar gidaje yana raguwa saboda gasa daga sababbin kamfanoni da suka shigo harkar. Kuma yanzu Urban Shelter ne ke ƙoƙarin samun sabbin dubaru na gine-gine na zamani da buƙatun kasuwa ga wasu masu siye daban-daban.

Wasu daga cikin sabbin shiga su ne kamfanoni masu zaman kansu da tsoffin ma’aikatansa suka kafa waɗanda suka koyi sana’ar, suka gina nasu kwastomomi, kuma ta wata hanya suka tara jari don canza ɓangaren harkokin gine-gine.

A wani ɓangare, asarar kasuwancinsa tana faruwa ne saboda sauya gwamnatocin Babban Birnin Tarayya Abuja masu amfani da manufofi daban-daban game da tsarin gidaje da amfani da filaye.

Fiye da shekaru goma, gwamnatocin baya sun fi son bayar da filaye ga kamfanoni masu gine-gine gidaje maimakon ɗaiɗaikon mutane.

Amma a ƴan shekarun baya-bayan nan, filayen da za a iya gina rukunin gidaje sun ƙare a hannun wasu mutane da kamfanoni da ba su da kuɗi ko damar samun bashi don manyan ayyukan gidaje ga masu matsakaicin matsayi. 

Maimakon haka, suna sayar da ƙananan yankuna na filin da aka ware, a zahiri suna tallata su a tituna. Wannan yana bayyana ƙarancin gidaje a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Malam Aliyu, wanda ke gab da cika shekaru 80, yana da kyakkyawan tarihin aiki da ya gina tsawon shekaru da dama a ɓangaren banki, kasuwanci, aikin gwamnati, da siyasa.

Kafin ya shiga harkokin siyasa a farkon shekaru 90, muƙamin gwamnati na ƙarshe da ya riƙe shi ne matsayin daraktan gudanarwa na babban bankin banƙasa masana’antun Nijeriya, wanda yanzu ake kira ‘Bank of Industry’. 

A cewarsa, ya haɓɓaka wani fili da gwamnati ta ba shi a Ɓictoria Island da ke Legas, sannan daga baya ya sayar da shi da tsada. Wannan ne ya sa shi ya fara harkokin gina gidaje da kuma yin tasiri.

Manya masu kuɗi na son ƙarin kuɗaɗe da tasiri da jin dadin rayuwa. Matsakaicin talakawa na son kaɗan ne kawai fiye da abin da ya mallaka. Wannan ne giɓi da sabon masu gine-gine ke ƙoƙarin cikewa.

Shuaibu Shuaibu
+ postsBio
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Akwai Ayar Tabaya Kan Zuba Hannun Jarin Dala Miliyan 750 Na Yari
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Wa Tanimu Turaki Ke Fafutukar Karewa?

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga A Wani Ƙauyen Katsina

Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan Bindiga A Wani Ƙauyen Katsina

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.