ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wa Tanimu Turaki Ke Fafutukar Karewa?

by Shuaibu Shuaibu
4 weeks ago
Tanimu

Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP, Tanimu Turaki, a kullun yana damun INEC da jam’iyyar mai mulki da kuma ɓangaren shari’a.

Turaki ya yi aiki a matsayin ministan ayyuka na musamman a ƙarƙashin shugabancin Goodluck Jonathan. Da zarar ya maye gurbin Iliya Damagum, kusan ana masa kallon wanda zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP.

Amma akwai ayar tambaya game da wanda Turaki yake fafutukar karewa kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

ADVERTISEMENT

Shin Jonathan ne da haƙƙin da tsarin mulki na kaɗa ƙuri’a da a tsayar da shi a jam’iyyar PDP, wanda yake buƙatar a sanya shi a takardar kaɗa ƙuri’a don samun matsayi bayan 2027, arewa na da ɗan takara guda, kudu maso kudu, wanda Jonathan ke wakilta, ko masu zaɓe za su zaɓe shi?

Turaki na son Goodluck Jonathan ya samu takarar a zaɓen 2027. Jam’iyyar na son Jonathan ya yi takara har ta kai ga ta miƙa sunan tsohon shugaban ƙasa ga INEC.

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

An bai wa sauran jam’iyyun siyasa lambobi don su shigar da sunayen ƴan takararsu ta hanyar shafukan yanar gizo da hukumar zaɓe ta buɗe.

Fadar shugaban ƙasa da jam’iyyar APC mai mulki ba sa son tsohon shugaban ƙasa ya tsaya takara a zaɓen saboda wasu dalilai bayyanannu. Ko dai saboda yadda suke fassara sabbin hukuncin kotun ƙoli ko kuma kawai saboda rashin tabbas, sannan INEC ma ba ta son Jonathan ya tsaya takara zaɓen.

Hukumar zaɓe na cikin matsala game da takarar Jonathan. Ya zama zakaran gwajin dafi kan ƴancin INEC da raba iko, da kuma amincin tsarin zaɓe.

Ko Jonathan zai samu shiga takarar ko a’a yana sanya shari’a cikin mawuyacin hali. Kotun ƙoli ta ta yi watsar da ɓangaren PDP da ministan Abuja, Nyesom Wike ke goyon baya.

Ministan ya bayyana a fili, yana fafutuka ne don Shugaba Tinubu da APC da yankinsa na kudu maso yamma.

Amma a bayyane INEC na jiran hukuncin kotun ɗaukaka ƙara kafin yanke shawarar wane ɓangare na PDP zai fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

Duk da haka, babu wani wuhala na gane dalilin da ya sa Shugaba Bola Tinubu ba ya so Jonathan ya tsaya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Tsohon shugaban zai iya samun ƙuri’u masu yawa a yankin kudu maso kudu.

Abun takaici shi ne, akwai yiwuwar samun ƙuri’u masu yawa daga Peter Obi na jamƴyar NDC, wanda zai iya samun rinjaye a yankin kudu maso gabas kuma wataƙila ya hana APC samun kashi 25 cikin ɗari na ƙuri’un yankin.

Kamar yadda aka samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Obi na iya samun rinjaye na ƙuri’u daga yankin Tinubu na kudu maso yamma, wurin da shugaban ƙasa yake da ƙarfi.

Saboda haka, yayin da ƴan takara uku na kudu suka raba ƙuri’unsu a yankin kudu maso gabas da kodu maso yamma, da kudu maso kudu, ɗan takarar shugabancin ƙasa na ADC zai iya samun gagarumin rinjaye a yankin arewa.

Manyan ƴan takara huɗu daga yankuna huɗu na ƙasar na iya canza yadda APC ke lissafin zaɓe.

Tanimu
Shuaibu Shuaibu
+ postsBio
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Akwai Ayar Tabaya Kan Zuba Hannun Jarin Dala Miliyan 750 Na Yari
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

MASU ALAKA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Next Post
Tanimu

NPA Ta Samo Tallafin Dala Biliyan 1 Domin Aikin Zamanantar Da Tashoshin Jiragen Ruwan Ƙasar Nan

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.