ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Akwai Ayar Tabaya Kan Zuba Hannun Jarin Dala Miliyan 750 Na Yari

by Shuaibu Shuaibu
3 weeks ago

Bincike ya nuna cewa Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi talauci a Nijeriya. Akwai hujjoji masu yawa da ke nuna haka. Alamu daga jihar sun nuna haka, haka hukumar ƙididdiga ta ƙasa da kuma hukumomin ƙasa da ƙasa sun nuna haka.

Alamu sun nuna abu mara kyau na yadda ake samun tsaro da tashin hankali, ciki har ma da yawan ɗaliban da ke rubuta jarabawar WAEC a kowace shekara.

Amma hakan yana a takarda. Wasu ƴan Nijeriya da ke bincike don samun damar zuba jari sun fara tunanin akasin haka. Wasu har ma suna da tabbacin cewa Zamfara ce jihar mafi arziki a Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Su ne shugabannin kasuwanci masu ƙarfin zuba hannun jari a ɓangaren ma’adinai na Nijeriya da ke fuskantar matsaloli, musamman a Zamfara. Abin ake haƙa yawanci su ne zinariya, wanda ‘gram’ ɗaya kawai zai iya kai kimanin naira 200,000 a kasuwar duniya.

Bisa sayen hannun jari na dala miliyan 750 na Sanata Abdulaziz Yari a ‘Geregu Power’, wani ƙoƙari ne na daidaita yawan albarkatun da Zamfara take haƙowa a takarda, wanda ta kasance ɗaya daga cikin manyan masu samar da albarkatu a Nijeriya a ƴan shekarun nan yana nuna kawai bambancin tsakanin sashen hukuma da wasu ɓangarori wanda ba na hukuma na ba.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Wannan kaɗan ne daga cikin labari a tsakanin gwamnati da kasuwanci, mene ne dalilin da ya sa haƙar ma’adanai ke kasancewa mafi yawa a ɓangaren ba na hukuma ba, da kuma abin da kasuwancin kamfani ke nufi a jihar kamar Zamfara, inda Yari ya yi gwamna.

Rashin biyan bashin naira biliyan 40 da Geregu Power ta yi ya sa masu zuba jari biyu cikin matsala. Ɗaya ya kasance babban ɗan kasuwa a Nijeriya, mai zuba jari a fannoni da dama, yayin da ɗayan kuwa shi ne ɗan siyasa mai matuƙar tasiri a duniya.

Ɓangaren wutar lantarki na Nijeriya na da nauyin bashi mafi girma a kowace masana’antu, har ya kai na tiriliyoyi naira. Ko gwamnatin tarayya ma ba ta iya biyan bashinta. Maimakon haka, ta nemi amfani da takardun bashi da gwamnati ke tallafawa don samun kudinsu.

Wannan ya bayyana dalilin da ya sa attajiri mai zubu jari, Femi Otedola, zai so ya sayar da hannun jarinsa gaba ɗaya. A watan Disamba 2025, ya sayar da hannun jarinsa a Geregu Power ga kamfanin Sanata Abdulaziz Yari, Ma’am Energy, kimanin dalar Amurka miliyan 750.

Bayan watanni shida, Yari ya karɓi shugabancin gudanar kulawar kamfanin Geregu Power. Kasancewarsa na iya zama amfani ga Geregu. A matsayinsa na ɗan siyasa mai tasiri, Yari yana da ƙwarewa wajen sa gwamnati ta biya bashin da kuma mayar da basussukan Paris Club a madadin jihar.

Amma har yanzu akwai tambayoyi game da ko Yari ya gudanar da bincikensa yadda ya kamata, ko yana da masu ba shi shawarar kan harkokin kuɗi, ko hukumomi sun ba Geregu tabbacin biya, ko kuma Yari kawai ya yanke shawarar zuba kuɗi mai yawa ba tare da yin tambayoyi ba.

Matsayin bashin a sashen wutar lantarki da Geregu ya fitar, abubuwa ne da aka sani a bainar jama’a.

Shugabancin kamfanin ta ba da bayani, tana cewa tana ƙoƙarin ganin ta kwantar da hankalin masu hannun jari, da masu kula da harkokin jari da kuma jama’a.

Bugu da ƙari, shugabancin kamfanin ya ce sun gudanar da cikakken bincike dukkan mu’amalolin kamfanin da basussuka, alƙawuran aiki da kuma tasirin kuɗi.

Amma babu abin da ke cikin bayanin, daga ƙwarewa a ɓangaren wutar lantarki a ƴan shekarun nan, ko daga Geregu Power da kansa ya bayyana dalilin da ya sa Sanata Abdulaziz Yari ya taɓa tunanin cewa jarinsa na dala miliyan 750 zai zama mai riba.

Shuaibu Shuaibu
+ postsBio
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Wa Tanimu Turaki Ke Fafutukar Karewa?
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post

Dattawan Borno Sun Roƙi Tinubu Da Zulum Su Ceto Mutane 116 Da Aka Sace

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.