Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce matasa ’yan Nijeriya sama da miliyan 9.32 ne suka yi rajista da ita gabanin babban zaɓen 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja, yayin ƙaddamar da jakadun matasa tara na INEC.
Kwamishinar INEC, Rhoda Gumus, ce ta wakilce shi a wajen taron.
Amupitan ya ce adadin ya nuna muhimmiyar rawar da matasa za su iya takawa a harkokin zaɓe da dimokuraɗiyya.
Ya ce naɗa jakadun matasan na daga cikin matakan da hukumar ke ɗauka domin ƙara kusantar matasa da kuma samar musu da sahihan bayanai kan harkokin zaɓe.
Ya buƙaci jakadun da su wayar da kan masu zaɓe, su ƙarfafa matasa su shiga harkokin zaɓe cikin lumana, tare da taimakawa wajen yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya game da zaɓe.
An zaɓi jakadun tara ne daga masana’antar nishaɗi, ciki har da ’yan fim, mawaƙa da ’yan wasan barkwanci.
A wani labarin kuma, INEC ta miƙa Takardar Shaidar Nasara ga Kallamu MaiJama’a, wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na mazaɓar tarayya ta Gombe/Kwami/Funakaye da aka gudanar ranar 19 ga watan Satumba, 2026.














