Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta cire kusan rajistar masu zaɓe miliyan 1.5 da aka gano suna ɗauke da kura-kurai ko alamun rashin bin ƙa’ida daga kundin rajistar masu zaɓe na ƙasa, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan ranar Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026, lokacin da ya karɓi tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya ƙarƙashin jagorancin wakilinta na musamman a Yammacin Afirka da yankin Sahel, Leonardo Santos Simão, a shalƙwatar hukumar da ke Abuja.
Amupitan ya ce hukumar ta gano waɗannan bayanan ne ta hanyar amfani da fasahar tantance bayanan masu zaɓe, a wani yunƙuri na tsaftace kundin rajistar da kuma tabbatar da sahihancinsa. Ya bayyana cewa INEC na ci gaba da gudanar da aikin tantancewa da sauraron ƙorafe-ƙorafe kafin kammala kundin rajistar.
Hukumar ta kuma bayyana cewa adadin masu zaɓe da ke cikin kundin rajistar ƙasar ya haura miliyan 103, inda matasa masu shekaru 18 zuwa 34 suka kai kusan kashi 29 cikin 100. Amupitan ya ce INEC na ƙarfafa amfani da na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS da kuma shafin IReV domin inganta gaskiya da sahihancin zaɓe.
INEC ta tsara fitar da kundin rajistar masu zaɓe na ƙarshe a ranar 15 ga Disamba, 2026. Wannan mataki na zuwa ne bayan hukumar ta gano bayanan rajistar da take da shakku kansu, ciki har da waɗanda ake zargin an ƙirƙira da hotunan AI ko kuma aka yi musu sauye-sauye ba bisa ƙa’ida ba.














