Gwamnatin Tarayya ta bayyana hanyoyi shida masu sauƙi da masu amfani da bankin zamani na ALAT By Wema Bank za su bi domin tantance cancantarsu da karɓar tallafin Naira 50,000 ƙarƙashin shirin tallafin gaggawa na NERSI, ba tare da buƙatar zuwa banki ba.
Shirin, wanda Ma’aikatar Jinƙai da Rage Talauci ta Tarayya ke gudanarwa, na da manufar tallafa wa gidaje masu ƙaramin ƙarfi da waɗanda tsadar rayuwa ta shafa. ALAT By Wema Bank na ɗaya daga cikin hanyoyin da gwamnati ta amince da su domin rarraba kuɗaɗen tallafin ga waɗanda suka cancanta.
Ga matakan da masu amfani da ALAT By Wema Bank za su bi:
Na farko, su shiga manhajar ALAT ta wayoyinsu.
Na biyu, su nemo sashin tallafin NERSI.
Na uku, su zaɓi zaɓin tantance cancanta.
Na huɗu, su shigar da bayanan da ake buƙata domin tantance su.
Na biyar, idan sun cancanta, su tabbatar da buƙatar karɓar tallafin.
Na shida, za a saka Naira 50,000 a asusunsu bayan kammala tantancewa da amincewa.
Gwamnati ta bayyana cewa za a zaɓi waɗanda za su amfana ne bisa sahihan bayanan da ke cikin rajistar ƙasa, tare da la’akari da halin tattalin arziƙin gidaje.
Mallakar asusun ALAT kaɗai ba ya tabbatar da cewa mutum zai samu tallafin, domin akwai tsarin tantance cancanta kafin a biya kuɗin.
An kuma shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan da masu damfara, kada su biya kuɗin rajista ko na taimakon karɓar tallafi, ko kuma su bai wa wani lambar sirrin asusu, OTP ko bayanan tsaro.
Tallafin kyauta ne, kuma waɗanda suka cancanta ne kawai za su amfana da shi.














