Yayin da Nijeriya ke tunkarar babban zaɓen 2027, rahotannin hare-hare kan ’yan siyasa, musamman ’yan takarar jam’iyyun adawa, na ƙara jawo hankalin jama’a kan matakan tsaro da kuma ’yancin gudanar da harkokin siyasa cikin lumana.
A cikin watannin baya-bayan nan, an samu rahotannin hare-hare kan ayarin motocin wasu ’yan siyasa a jihohin Benue da Cross River.
Waɗannan lamura sun sake buɗe muhawara kan rawar da jami’an tsaro da jam’iyyun siyasa za su taka wajen hana tashin hankali a lokacin kamfen.
Hare-haren kan ayarin motocin Peter ObiA ranar 8 ga Satumba, 2026, an ruwaito cewa wasu matasa sun tare ayarin motocin Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigerian Democratic Congress (NDC), a kan hanyar Gboko da ke Makurdi, Jihar Benue.
Rahotanni sun ce matasan sun yi wa motocin ayarin jifa da duwatsu, lamarin da ya hana Obi ci gaba da tafiya zuwa Yelwata.
’Yan sanda sun kama mutum 46 da ake zargi da hannu a lamarin, sai dai gwamnatin Jihar Benue ta musanta zargin cewa tana da hannu a harin.
Haka kuma, a ranar 4 ga Nuwamba, 2026, an sake kai hari kan ayarin motocin Obi a Calabar, Jihar Cross River, inda aka lalata gilashin wasu motoci da abubuwa masu kaifi.
A ranar 5 ga Nuwamba, ’yan sanda suka sanar da kama wani mutum mai shekaru 27 da ake zargi da hannu a harin.
Duk da cewa kama waɗanda ake zargi ba ya nufin an tabbatar da laifinsu, waɗannan rahotanni sun ƙara jawo tambayoyi kan yadda ake kare ’yan siyasa yayin gudanar da harkokin kamfen.
Nauyin ’Yan sanda wajen kare ’yan takaraA ƙarƙashin Sashe na 14(2)(b) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, tsaro da jin daɗin jama’a na daga cikin manyan manufofin gwamnati.
Haka kuma, Sashe na 40 ya tabbatar da ’yancin jama’a na haɗuwa da kafa ko shiga jam’iyyun siyasa.
Bugu da ƙari, Sashe na 95 na Dokar Zaɓe ta 2026 ya ɗora wa kwamishinan ’yan sanda a jiha da Abuja alhakin samar da isasshen tsaro a tarukan siyasa da jerin gwanon jam’iyyu.
Wannan tanadi ya nuna cewa aikin ’yan sanda bai tsaya ga shiga tsakani bayan tashin hankali ya ɓarke ba.
Ya haɗa da ɗaukar matakan kariya domin tabbatar da gudanar da harkokin siyasa cikin lumana.
Sai dai, abin da ke buƙatar kulawa shi ne yadda ake aiwatar da wannan nauyi a aikace, musamman idan aka yi la’akari da rahotannin hare-haren da ake samu a wasu sassan ƙasar.
Alhakin jam’iyyun siyasaBaya ga jami’an tsaro, jam’iyyun siyasa da ’yan takara ma suna da rawar takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a lokacin kamfen.
Ana buƙatar shugabannin jam’iyyu su guji kalaman tunzura jama’a, barazana da amfani da ’yan daba wajen tarwatsa tarukan abokan hamayya.
Haka kuma, ya kamata su tabbatar da cewa magoya bayansu suna bin dokoki yayin gudanar da taruka da jerin gwanon siyasa.
A ranar 18 ga Agustan 2026, Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa ya shirya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin shugabannin jam’iyyu da masu neman takara domin rage tashin hankali a zaɓen 2027.
Sai dai, rattaba hannu kan yarjejeniyar kaɗai ba zai wadatar ba idan ba a bi ta da matakan tabbatar da bin ƙa’idoji da kuma hukunta waɗanda suka aikata laifukan siyasa ba.
Tasirin tashin hankali ga zaɓen 2027
Masana harkokin zaɓe da masu sa ido kan dimokuraɗiyya na kallon tsaro a lokacin kamfen a matsayin muhimmin ginshiƙi na sahihin zaɓe.
Idan aka bar hare-hare da barazanar siyasa ba tare da bincike da ɗaukar mataki ba, hakan na iya hana ’yan takara gudanar da kamfen cikin ’yanci, tare da rage damar jama’a na jin manufofin jam’iyyu daban-daban.
Haka kuma, yanayin rashin tsaro na iya sanyaya gwiwar mata, matasa da sauran masu rauni shiga harkokin siyasa saboda tsoron cin zarafi ko barazana.
Saboda haka, ana buƙatar ’yan sanda su binciki rahotannin hare-hare cikin gaggawa, tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban kotu.
Haka kuma, ya kamata a tabbatar da cewa kariyar da ake bai wa ’yan takara ba ta dogara da jam’iyyar da suke wakilta ba.
Shin za a tabbatar da tsaro ga kowa?Yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ci gaba, babban ƙalubale shi ne tabbatar da cewa bambancin ra’ayin siyasa ba ya zama sanadin kai hari, barazana ko hana wani ɗan takara gudanar da kamfen.
Hakan na buƙatar INEC, ’yan sanda, jam’iyyun siyasa da sauran hukumomin da abin ya shafa su ƙarfafa haɗin gwiwa wajen sa ido kan lamuran tsaro, karɓar ƙorafe-ƙorafe da kuma tabbatar da bin doka.
A ƙarshe, sahihancin zaɓe ba ya dogara da ranar kaɗa ƙuri’a kaɗai. Yana farawa ne tun lokacin da ’yan takara suka fara neman goyon bayan jama’a.
Saboda haka, yadda hukumomin tsaro za su kare dukkan ’yan takara da kuma tabbatar da ’yancin gudanar da kamfen zai kasance ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da za a sa ido a kai gabanin zaɓen 2027.














