Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da ƙoƙarin raunana jam’iyyar ADC bayan hukuncin kotu da ya rushe shugabancin jam’iyyar.
Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, ya bayyana hukuncin kotun na ranar Alhamis da ya rushe shugabancin Sanata David Mark a matsayin wani shiri na kawo cikas ga takararsa.
A cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, Daraktan Yaɗa Labarai na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ADC, ya fitar ranar Alhamis, Atiku ya ce hukuncin ya zo ne kwana ɗaya kacal bayan ɗimbin jama’a sun tarbe shi a Sakkwato yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa.
Ya yi zargin cewa an yi hukuncin ne domin raunana goyon bayan da yake da shi a Arewacin Nijeriya, yana mai cewa goyon bayansa bai tsaya iya yankin Arewa ba.
Atiku ya kuma nuna shakku kan ingancin hukuncin, inda ya ce wata babbar kotun tarayya ta taɓa yin watsi da ƙarar da ta ƙalubalanci shugabancin ADC ƙarƙashin Sanata David Mark.
Ya ce jam’iyyar za ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar sabon hukuncin.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci magoya bayan ADC su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda, yana mai cewa za su ci gaba da yaƙin neman zaɓe duk da hukuncin.
Ya ce yaƙin neman zaɓensu zai mayar da hankali wajen magance tsadar rayuwa da kuma sauƙaƙa wa ’yan Nijeriya halin ƙuncin tattalin arziƙi.














