ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Iyaye Suna Kokawa Kan Kuɗaɗen Da Suke Kashewa Kan Bikin Kammala Karatu

by Sulaiman
1 month ago
Iyaye

Yawancin makarantu masu zaman kansu a Nijeriya da akwai wani abu da aka ɓullo da shi,wanda ko shakka babu Iyaye basu jin daɗin shi saboda kuwa bayan biyan kuɗin makaranta mai tsada, kayan da ake sa wa domin zuwa mnakaranta da kuma littattafai na karatu, sai ga shi kuma ana fuskantar su Iyayen da ƙaruwar wasu buƙatu: da suka haɗa da ranar irin aikin da mutum yake son ya yi bayan ya kammala makaranta, ranar al’adu,liyafofin aji, bukukuwan ranar haihuwa, bayyana irin baiwa ko fasahar da Allah ya yi wa mutum,da kuma bukukuwan kammala makaranta.

Waɗannan abubuwan an ɓullo da su ne a matsayin wata dama ce, da yaro zai koyi karatu da kuma bunƙasar shi, sai dai kuma ta wani ɓangaren yadda ake ci gaba da amsar kuɗi lokaci zuwa lokaci sai abin ya zama wata babbar matsalar da ke damun su Iyayen yaran.

Yadda ake tafiyar da makarantu yanzu musamman ma zangon karatu na makaranta mai zaman kanta abin ya zama wani lamari ne da yake buƙatar Iyaye su samar da kayan sa wa, wani lokaci na gargajiya, ko kuma su bada kuɗi saboda yin wasu bukukuwan. Alal misali da za ayi bikin al’adun gargajiya, wadda za ta iya nuna ko ɗan/ ƴar wacce kabila ne ko /ce,yayin da ita kuma ita ranar irin aikin ake son yi hakan yana buƙatar wasu kayan sawa na musamman, kama (lab coats) irin rigar da masu aiki a ɗakin gwaji ke sawa, kayan da sojojin ke sa wa, ko kuma irin kayan sa wa da ƙwararru ke ke sa wa lokacin aiki a afis.

ADVERTISEMENT

Da yawa daga cikin waɗanda Iyayensu ke aiki da kuma suma da suka kasance ƴan tsaka-tsaki, nau’oin buƙatun sau da yawa ya kan zarce abubuwan da su ke yanke shawarar kashewa a zangon karatun bama kamar waɗanda suke da ƴaƴa da yawa da ke zuwa makaranta.

Bukukuwan kammala makaranta ko da ace a makaranta ta reno ne ko kuma ɓangaren Firamare, ko shakka babu abin ya kai wuce misali. Saboda kuwa makarantu sukan so ne Iyaye su biya kuɗaɗe masu yawa domin kuwa irin rigar da ake sa wa lokacin da aka kammala karatun, tana da matuƙar tsada lokacin, ko kuma su ɗauke nauyin samar da kayan shaye- shaye, da ciye – ciyen da za ayi a ranar.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

Iyaye

Akwai ma lokacin da ake sa su yara su koyi yadda ake wani abu da ake kira da suna Choreography wanda wani abu ne da ake jera shi daban- daban, wani irin motsi ne da za ayi da sassan jiki mai nau’i- nau’i wayancinsu duk rawa ce. Za kuma su fito ne waɗanda aka zaɓa su yi a gaban mutane a ranar, maganar gaskiya wani abu ne da yake buƙatar sai an tanaji kuɗi da kuma nau’oin kayan sawar da za ayi amfani da su.

Irin waɗannan bukukuwan duk da suke na jin daɗi ne ba a yin maganarsu ranar da ake sa yaro koƴaƴa a makaranta saboda kuwa kowane biki da za ayi da akwai kuɗaɗen da suke biye masu baya.

Duk da ya ke dai ire-iren abubuwan suke taimakawa da ta ke kasancewa ba wadda za a iya kiman ta,ta ba wajen sani ilimin al’adu su yaran suke koya ba, sai kuma babban lamari ga sanin yadda za ayi hulɗa a gargajiyan ce. Sai dai kuma wani hanzarin da ya kasance ba gudu bane, domin kuwa ba ayi la’akari da yadda lamarin halin kuɗaɗen da su Iyaye ne ke biya.

Yawancin su makarantu basu samar da hanyoyi da za abi har a samu bin wata ko wasu domin a samu cimma buƙatun irin su nau’oin bukukuwa ba, ko kuma su bada dama ta tautaunawa akan kuɗaɗen da za a kashe ba.Maimakon haka ma,da akwai abinda ba za ayi maganar shi ba amma kuma ana sa ran su Iyaye su bada suka yi yadda ake buƙata, wanda kuma ba a san irin matsalolin da su Iyaye su ke fuskanta ba,duk kuwa da kowa ya san irin matsin tattalin arziki da ƴan Nijeriya suke fuskanta, amma Iyaye ko da abin zai shafi yadda suka kasafta kashe kuɗaɗen da suke hannunsu, duk da hakan, hakanan za su yi haƙuri su biya, saboda ba su son a bar ƴaƴansu su kasance Sanuwar ware, ko su ƴaran su ga tamkar an ba su a sashen ƴaƴan Bora ne.

Wani abu kuma wanda yake daban ne,abubuwan da ake yi lokacin bukukuwan kammala karatun sun kasance dole ne sai an yi su, yaran da basu biyan kuɗin rigunan da ke sawa ba na kammala makaranta, ana ce masu ne, kada su kasance kusa da azuzuwa, babu kuma wata maganar su sa ran za a basu wani maƙulashe ko hotunan da za a ɗauka tare da su.

Ita kuwa Mrs.Christine Edeme, matar aure da take da ƴaƴa huɗu da suke makaranta a Jabi, ta bayyana cikin halin damuwar da take ne, sanadiyar irin ɗawainiyar da ake ɗorawa kan Iyaye.Cewa ta yi “Ina tunanin duk waɗannan abubuwan ba dole ba ne.

Kamar ƴaƴa na a wannan zangon karatun,su huɗu a can makarantar. Dukkanin abubuwan in aka haɗa su da kuɗaɗen makaranta, ba wani abinda zai dame ni bane.

Sai dai kuma wani abu muna ji a jikin mu a matsayin mu na Iyaye, da muke ta faɗi- tashi domi mu samu kuɗin, mu je can domin mu ga wannan ko wancan muna ta fafutuka.

Amma wani lokaci bana barin su kasance cikin harkokin domin kuwa a wasu daga cikin mu ba ƙaramar damuwa ba ce, domin kuwa wani lokacin bani da kuɗin da zan iya biya saboda a samu damar yin su bukukuwan. Ba wai bani buƙatar su riƙa kasance a cikin abubuwan da ake yi ba ne ,amma bubuwa suna da tsada.Ga irin mu da muke da ƴaƴa uku,huɗu, ko ma ƴaƴa biyar, ba ƙaramin abu ba ne. Halin yanzu ina da abubuwan da ake ƴaƴa na su ɗinka: kayan gayu irin ɗaya ke nan kawai,na ɗinka riguna farare biyu da wanduna biyu, na kashe ku san Naira 15,000 akan kowane mutum ɗaya.Don haka su biyu, Naira 30, 000 ke nan.

Sun ce mana mu kawo abinci wanda yara za su yi amfani da shi a azuzuwansu, wannan kuma ya shafi dukkan ƴaƴana uku. Zan kashe kusan Naira 80,000 saboda wani abu ɗaya kawai. Wannan ba wasu liyafofi bace ta aji, ko kuma lamarin wasanni na tsakanin gida- gida na makarantar, da dai sauransu. Wannan ai bai dace ba.”Wata mata da take ma’aikaciya ce da ake kira da suna, Faɓour Akaangee, cewa abin ya zame mata dole ne sai ta bar yin wasu abubuwa domin tabbatar da ƴa’anta sun samu biyan buƙatun makaranta dukkuwa da yake ana fuskantar matsin tattalin arziki.“Duk mun san cewa abin yana da wuya ban san kuma abinda wasu Iyayen suke fuskanta ba, amma ga re ni wannan lamarin yana da matuƙar wuya da wahala.

Ƴaƴa na biyu sun kammala makaranta, gaskiya ina cikin wani mawuyacin hali.Babu wanda ke taimaka mani a shago ne a halin da ake ciki babu wani mai taimaka ma ni, koda wane lokaci idan bani nan to za a same ni a can, abin ba ƙaramar wahalar da ni yake yi ba. Idan suka zo gida da maganar buƙatar wani abu kamar kuɗaɗen bukukuwan kammala karatu,ko ga irin kitson da ake son ayi ko sutura/kayan za ayi amfani da su, ya kamata na sayi su abubuwan.

Ba ni da kuɗin, sai dai kuma wani lamari bani da wani zaɓi.Kowa ya san me ake nufi da ace yau mutum yana da ƴaƴa, ba ni son su fita har ma a riƙa masu kallon da bai kamata ba.Babu wani zaɓi dole ne na yi abinda ya dace.Maganar fuskantar duk wani abinda ya taso dangane da karatunsu ita ce ta kamata, ko wane lokaci dai su kasance basu cikin damuwa idan suna cikinƴan’uwansu yara ƴan makaranata.”

“Tsakanin biyan kuɗin makaranta (waɗanda ko wane lokaci ana ƙara su ko kuma sa ido ko lura da lamarin da kowace rana a samu ɗaukar nauyin abincin rana na yara.Rigar da ake sa wa ranar bikin kammala makaranta Naira 10,000, sai ɗinka kayan sa wa na gargajiya, ga kuma bada gudunmawa wajen kayan shan da za ayi amfani da su lokcin liyafar azuzuwa. Ma fi ƙaranci kuɗin da Tela zai amsa Naira 5000. Ina hanin su yara za su ji daɗi ne, sai dai kuma gare mu Iyaye abin yana da matuƙar wuya, gaskiya da akwai wuya cewar John Idowu mutumin da yake da ƴaƴa uku.”

Iyaye
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang
  • Sulaiman
    Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris
  • Sulaiman
    Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu
  • Sulaiman
    Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

MASU ALAKA

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Labarai

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Iyaye
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Iyaye
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Next Post
Samfurin Kirkirarriyar Basira Ta AI Na Sin Ya Samu Karbuwa Sosai A Harkokin Tattalin Arziki Na Zahiri

Samfurin Kirkirarriyar Basira Ta AI Na Sin Ya Samu Karbuwa Sosai A Harkokin Tattalin Arziki Na Zahiri

LABARAI MASU NASABA

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Iyaye

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Iyaye

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026
Iyaye

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.