ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 2, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jami’an Sin Za Su Ziyarci Gabas Ta Tsakiya Da Sauran Yankuna Domin Inganta Zaman Lafiya Da Tattaunawa

by CGTN Hausa
49 minutes ago
Sin

A yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Inda a gun taron, ta gabatar da wasu bayanai game shirin kasar Sin na tura manzon musamman, da wakilin musamman don ziyartar kasashe dake Gabas ta Tsakiya musamman yankunan Gulf da na Bahar Maliya, da kuma Kahon Afirka.

Mao ta bayyana cewa, wakilin musamman na gwamnatin Sin kan harkokin Afirka zai ziyarci kasashen Habasha, da Djibouti, da Masar a farko zuwa tsakiyar watan nan na Nuwamba, yayin da wakilin musamman na Sin kan harkokin yankin Kahon Afirka zai ziyarci kasar Eritrea a farkon watan na Nuwamba.

Jami’ar ta ce wadannan ziyarce-ziyarce na da nufin inganta zaman lafiya da tattaunawa, da rage tashin hankali, da kuma taka rawa mai amfani wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan.

ADVERTISEMENT

Bugu da kari, dangane da ziyarar da shugaban kasar Gabon, Brice Clotaire Oligui Nguema, zai gudanar a kasar Sin nan ba da jimawa ba, Mao Ning ta bayyana cewa, Sin na fatan yin aiki tare da Gabon, bisa damar wannan ziyara don daukaka dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki, tare da bayar da karin gudummawa wajen gina kyakkyawar makoma ta bai-daya ta Sin da Afirka a sabon zamani.

Game da amincewar da kwamitin kwance damara da tsaron duniya na MDD ya yi, kan wani kuduri mai taken “Inganta amfani da hadin gwiwar kasa da kasa ta hanyar zaman lafiya a fagen tsaron kasa da kasa”, wanda Sin ta gabatar a babban taron MDD karo na 81, Mao Ning ta bayyana cewa, aiwatar da wannan kuduri wani muhimmin bangare ne na kokarin Sin kan aiwatar da shawarwarin tsaron duniya.

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Xi Jinping Ya Ba Da Umarni Game Da Aikin Daidaita Yanayin Rawayan Kogi

Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Matan Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Harkokin Raya Kasa?

Mao Ning ta kuma sanar da cewa, mamba a ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai karbi bakuncin taron ministocin harkokin waje karo na 11 na hadin gwiwar Lancang-Mekong a birnin Beijing, daga gobe Talata 3 zuwa Laraba 4 ga watan nan na Nuwamba. (Safiyah Ma)

Sin
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Shugaba Xi Jinping Ya Ba Da Umarni Game Da Aikin Daidaita Yanayin Rawayan Kogi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Matan Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Harkokin Raya Kasa?
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Bautawa Jama’a-Mabudin Fahimtar Ayyukan JKS
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ma’aunin JKS Na Zabar Mambobi Da Jami’anta

MASU ALAKA

Shugaba Xi Jinping Ya Ba Da Umarni Game Da Aikin Daidaita Yanayin Rawayan Kogi
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Jinping Ya Ba Da Umarni Game Da Aikin Daidaita Yanayin Rawayan Kogi

November 2, 2026
Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Matan Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Harkokin Raya Kasa?
Daga Birnin Sin

Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Matan Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Harkokin Raya Kasa?

November 2, 2026
Bautawa Jama’a-Mabudin Fahimtar Ayyukan JKS
Daga Birnin Sin

Bautawa Jama’a-Mabudin Fahimtar Ayyukan JKS

November 2, 2026
Next Post
Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Waɗanda Aka Sace A Taraba

Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Yayin Karɓar Kuɗin Fansa A Nasarawa

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Waɗanda Aka Sace A Taraba

Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Yayin Karɓar Kuɗin Fansa A Nasarawa

November 2, 2026
Jami’an Sin Za Su Ziyarci Gabas Ta Tsakiya Da Sauran Yankuna Domin Inganta Zaman Lafiya Da Tattaunawa

Jami’an Sin Za Su Ziyarci Gabas Ta Tsakiya Da Sauran Yankuna Domin Inganta Zaman Lafiya Da Tattaunawa

November 2, 2026
Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 

Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Ofishin Kamfen Na ADC

November 2, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutane Biyu Bisa Laifin Kisan Kai A Kano

November 2, 2026
Shugaba Xi Jinping Ya Ba Da Umarni Game Da Aikin Daidaita Yanayin Rawayan Kogi

Shugaba Xi Jinping Ya Ba Da Umarni Game Da Aikin Daidaita Yanayin Rawayan Kogi

November 2, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Wayoyin Lantarki A Gombe

November 2, 2026
Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Matan Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Harkokin Raya Kasa?

Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Matan Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Harkokin Raya Kasa?

November 2, 2026
Tinubu

Zama Shugaban Nijeriya Babbar Ni’ima Ce Daga Allah — Tinubu

November 2, 2026
Bautawa Jama’a-Mabudin Fahimtar Ayyukan JKS

Bautawa Jama’a-Mabudin Fahimtar Ayyukan JKS

November 2, 2026
‘Yan Ta’adda Sun Yi Wa Tawagar ’Yansanda Kwanton Ɓauna A Hanyar Zamfara

‘Yan Ta’adda Sun Yi Wa Tawagar ’Yansanda Kwanton Ɓauna A Hanyar Zamfara

November 2, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.