ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 2, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zama Shugaban Nijeriya Babbar Ni’ima Ce Daga Allah — Tinubu

by Sulaiman
4 hours ago
Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana zama shugaban Nijeriya a matsayin wata babbar ni’ima da Allah ya yi masa, yana mai cewa zai yi amfani da damar wajen yi wa ƙasa hidima da samar da ci gaba da wadata.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan ziyarar ibadar Umrah da ya kai ƙasar Saudiyya, inda ya samu damar shiga cikin Ƙa’aba mai alfarma a Makka tare da jagorantar tawagar Nijeriya wajen yin addu’a.

A cewar sanarwar da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ƙasar ya ce ya roƙi Allah ya ba shi hikima da juriyar ci gaba da yi wa ’yan Nijeriya hidima.

ADVERTISEMENT

Ya kuma bayyana cewa ikon mulki amana ne daga Allah, don haka wajibi ne shugabanni su yi amfani da shi cikin tawali’u da adalci wajen yi wa al’umma hidima.

Tinubu ya ce yana da yakinin cewa tattalin arzikin Nijeriya ya fara fita daga mawuyacin halin da ya shiga, yana mai cewa ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar ya samu ƙarfi.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Ofishin Kamfen Na ADC

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutane Biyu Bisa Laifin Kisan Kai A Kano

Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen samar da makoma mai kyau ga matasa ta hanyar zuba jari a ci gabansu.

Shugaban ya kuma gode wa Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, bisa damar da suka ba shi da tawagarsa ta shiga cikin Ƙa’aba domin gudanar da addu’o’i.

Ya bayyana damar a matsayin wata muhimmiyar kyauta ta tarihi da ba zai manta da ita ba, wadda kuma ke nuna kyakkyawar alakar Najeriya da Saudiyya.

Tinubu
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Yayin Karɓar Kuɗin Fansa A Nasarawa
  • Sulaiman
    Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Ofishin Kamfen Na ADC
  • Sulaiman
    Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutane Biyu Bisa Laifin Kisan Kai A Kano
  • Sulaiman
    ’Yansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Wayoyin Lantarki A Gombe

MASU ALAKA

Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 
Manyan Labarai

Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Ofishin Kamfen Na ADC

November 2, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga
Manyan Labarai

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutane Biyu Bisa Laifin Kisan Kai A Kano

November 2, 2026
Kano: An Kama ’Yan Kasuwa Bisa Zargin Ƙoƙarin Sauya Ranar Ƙarewar Amfanin Wata Madara
Manyan Labarai

Kano: An Kama ’Yan Kasuwa Bisa Zargin Ƙoƙarin Sauya Ranar Ƙarewar Amfanin Wata Madara

November 2, 2026
Next Post
Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Matan Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Harkokin Raya Kasa?

Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Matan Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Harkokin Raya Kasa?

LABARAI MASU NASABA

Bangaren Jigilar Kayayyaki Na Sin Ya Samu Tagomashi A Rubu’i 3 Na Farkon Bana

Bangaren Jigilar Kayayyaki Na Sin Ya Samu Tagomashi A Rubu’i 3 Na Farkon Bana

November 2, 2026
Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Waɗanda Aka Sace A Taraba

Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Yayin Karɓar Kuɗin Fansa A Nasarawa

November 2, 2026
Jami’an Sin Za Su Ziyarci Gabas Ta Tsakiya Da Sauran Yankuna Domin Inganta Zaman Lafiya Da Tattaunawa

Jami’an Sin Za Su Ziyarci Gabas Ta Tsakiya Da Sauran Yankuna Domin Inganta Zaman Lafiya Da Tattaunawa

November 2, 2026
Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 

Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Ofishin Kamfen Na ADC

November 2, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutane Biyu Bisa Laifin Kisan Kai A Kano

November 2, 2026
Shugaba Xi Jinping Ya Ba Da Umarni Game Da Aikin Daidaita Yanayin Rawayan Kogi

Shugaba Xi Jinping Ya Ba Da Umarni Game Da Aikin Daidaita Yanayin Rawayan Kogi

November 2, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Wayoyin Lantarki A Gombe

November 2, 2026
Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Matan Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Harkokin Raya Kasa?

Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Matan Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Harkokin Raya Kasa?

November 2, 2026
Tinubu

Zama Shugaban Nijeriya Babbar Ni’ima Ce Daga Allah — Tinubu

November 2, 2026
Bautawa Jama’a-Mabudin Fahimtar Ayyukan JKS

Bautawa Jama’a-Mabudin Fahimtar Ayyukan JKS

November 2, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.