A baya bayan nan ne hukumar kula da samar da abinci da raya aikin gona ta MDD FAO, ta gudanar da bikin karrama “Hazikan Mata” a fannin samar da abinci da raya yankunan karkara. Daga cikin mata 609 da aka zaba daga kasashe 131 mambobin hukumar, mata 100 ne suka samu lambar karramawar, kuma mata 3 daga kasar Sin da suka hada da Yin Yuzhen da Dong Minfang da Yu Jinxiu na daga cikinsu, lamarin da ya sa Sin ta zama kasar da ta samu adadi mafi yawa na matan da aka karrama.
Dukkan wadannan mata sun bayar da gudunmuwa matuka a bangrori daban daban, kama daga wadda ta shafe tsawon shekaru 40 tana yaki da hamada, sai wadda ta bar aiki mai gwabi a birni ta koma kauye domin bunkasa samar da hatsi da zamanantar da aikin gona, da kuma wadda ta shafe tsawon shekaru 20 tana raya wata fasahar gargajiya.
A zamana da ziyarce-ziyarcen da na yi a kasar Sin, na gani da idanuna yadda mata a bangarori daban-daban na rayuwa ke taka rawar gani wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da zamantakewa. Kuma wadannan mata sun hada da wadanda suka yi karatun boko da wadanda ba su yi ba. Ko mene ne dalilin da ya sa matan kasar Sin ke taka rawar gani a harkokin raya kasa?
Salon shugabanci shi ne kashin bayan duk wani ci gaba da nasarorin da Sin ke samu. Kyakkyawan kudurin shugabanci shi ne ya kai ga daidaita manufofin gwamnati da tsare-tsaren raya tattalin arziki da zamantakewa, ta yadda za su dace da yanayin karkara da ayyukan karfafa gwiwar mata. A kasar Sin, mata sun tashi daga masu karbar tallafi kadai, inda suka zama wadanda ake damawa da su a harkokin raya tattalin arziki. Wani muhimmin batu shi ne, karkashin manufofin gwamnati na raya kasa da bunkasa zamantakewa, babu wariya- mata na samun duk wata dama da ke akwai, kamar takwarorinsu maza. Misali, ana samar da dimbin hanyoyin bayar da rance domin bunkasa sana’o’i ga mata. Kuma ba a bar su haka kawai ba.
Haka kuma, ana bibiyarsu ta yadda za a tabbatar da ba su sake komawa kangin talauci ba. Yayin da nake ziyara a lardim Guizhou a shekarun baya, wata jami’a ta shaida min cewa “ a nan (kasar Sin) muna daukar kawo karshen fatara a matsayin mafarin aikinmu.” Watau kawo karshen talauci, ba ya nufin aiki ya tsaya, ana ci gaba da gudanar da ayyuka da tsara dabaru domin karfafa nasarar da aka samu don tabbatar da dorewarta. Baya ga haka, ana tsara shirye-shiryen horar da mata ne ta yadda za su dace da yanayinsu, watau kasancewarsu masu kula da gida da bayar da tarbiyya.
Zuwa shekarar 2020, sama da mata miliyan 10.2 da a baya suka yi fama da talauci ne suka samu horon sana’o’i daban daban. Karkashin irin shirye-shiryen, an bullo da sana’o’i kamar na raya fasahohin gargajiya irin wadanda mata za su iya yi a gida, akwai kuma cinikayya ta intanet da ma yadda za su tallata da sayar da kayayyakinsu ta kafar intanet ba tare da sun bar gidajensu ba da sauransu.
Hakika dabarar karfafa wa mata gwiwa ta kasar Sin da ma yadda mata suke taka rawar gani, abun koyi ne ga kasashen duniya.Yayin da matan kasar Sin ke dukufa wajen kyautata rayuwarsu da zama masu dogaro da kansu, suna samun goyon baya da tallafi daga kyakkyawan shugabanci irin na gwamnatin Sin. Wannan ya nuna irin hadin gwiwar da ke tsakanin al’umma da gwamnati da kuma irin kishin kasa da ke cikin zukatan Sinawa.














