Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umarni a kwanan baya, kan aikin ci gaba da daidaita yanayin da Rawayan Kogi, ko kuma kogin Huanghe da Sinanci ke ciki, inda ya ce, ya kamata a tsaya tsayin daka kan manufar tsimin ruwa, da samun daidaito tsakanin ayyukan raya tattalin arziki da kare muhallin halittu, da kokarin gado da yayata al’adu mai alaka da kogin, don haifar da alfanu ga zuriyoyi na gaba.
Baya ga haka, shugaban ya ce, dimbin nasarorin da aka samu bisa kokarin daidaita yanayin kogin Huanghe a karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, cikin shekaru 80 da suka gabata, sun nuna fifikon tsarin siyasa na Gurguzu da ake bi a kasar ta Sin.
An sanar da wannan umarni na shugaba Xi ne a wani taron kyautata yanayin da kogin Huanghe ke ciki, wanda ya gudana a yau Litinin a birnin Zhengzhou na kasar Sin. (Bello Wang)














