Kwamitin kolin JKS ya fitar da sanarwa game da zaben wakilan babban taro na 21 na wakilan mambobin jam’iyyar, yayin da yake shirya ayyuka masu ruwa da tsaki.
A cewar sanarwar da aka fitar yau Asabar, sashen kula da shirye-shirye na kwamitin kolin ya riga ya tsara shirye-shiryen zaben dalla dalla.Yayin zamansa na 5 da ya gudana a karshen watan Oktoba ne kwamitin kolin JKS na 20, ya yanke shawarar cewa, jam’iyyar za ta gudanar da babban taro na 21 na wakilan mambobinta a rabi na biyu na shekarar 2027, a birnin Beijing.
Babban taron na zuwa ne a lokaci mai muhimmanci da jam’iyyar ke aiki domin cimma zamanantarwa ta gurguzu da kuma kokarin cimma burikan shekaru 100 na biyu. Taron zai kasance mai matukar muhimmanci, kasancewarsa mai matukar tasiri a siyasance ga jam’iyyar da ma kasar. Sanarwar ta ce zaben wakilai mahalarta taron, zai shimfida wani tubali mai muhimmanci ga nasarar taron.
Jimilar wakilai 2,360 ne za a zaba daga mazabu 38 da ke fadin kasar, domin halartar babban taron na kasa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














