Dan sama jannati na kasar Pakistan zai bi tawagar ‘yan sama jannatin kasar Sin ta Shenzhou-24, a matsayin mai kula da kayayyaki. Bayan kammala zagaye na gajeren lokaci a sararin samaniya, ‘dan sama jannatin na kasar Pakistan zai dawo doron kasa cikin kumbon Shenzhou-23.
Karbar ‘dan sama jannati bako na farko da cibiyar binciken sararin samaniya ta Sin za ta yi, zai kasance karo na farko da ‘yan sama jannati Sinawa da ‘dan kasar waje za su gudanar da aiki tare a tarihin ayyukan sama jannati na kasar Sin.
A watan Fabrerun 2025 ne Sin da Pakistan suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da ta shafi zaben ‘dan sama jannati da bayar da horo da tashi zuwa tashar binciken samaniya ta Sin, a birnin Islamabad, lamarin da ya kaddamar da zaben ‘dan sama jannati a hukumance daga kasar Pakistan.
Bayan ayyukan zabe da tantancewa a matakai 3, an zabi ‘yan sama jannati biyu na kasar Pakistan. Kuma bayan kammala horo da tantancewa a kasar Sin, daya daga cikinsu zai shiga cikin tawagar kasar Sin ta ‘yan sama jannati da za ta tashi zuwa sararin samaniya, yayin da dayan zai zaman jira a matsayin mataimaki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)













