Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta Sin ta sanar a yau Asabar cewa, kasar na matukar adawa da takunkuman da Amurka ta yi gaban kanta wajen kakaba wa kamfanonin kasar Sin, tana cewa matakin ya saba wa dokokin kasa da kasa da ma ka’idojin huldar kasa da kasa.
Kakakin ma’aikatar ce ta bayyana haka lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai game da matakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, na sanar da kakaba takunkumai kan wasu kamfanonin Sin 2 a ranar Alhamis.
Rahotanni na cewa, wannan shi ne karo na farko da Amurka ta sanya wa kamfanonin Sin takunkumi bisa dalilan da suka shafi kasar Cuba.
A cewar kakakin, kwanakin baya-bayan nan, Amurka ta matsa kaimi wajen sanya takunkumai da yunkurin danne kasar Sin, tare da daukar matakan nuna mata wariya, wadanda ke lahanta hakkoki da muradun kamfanonin Sin. Ta ce matakan sun yi hannun riga da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, haka kuma suna haifar da tsaiko ga kwanciyar hankalin dangantakar cinikayya da tattalin arziki da ke tsakanin Sin da Amurka.
A don haka a cewar kakakin, Sin na bukatar Amurka ta gyara kuskurenta ba da jimawa ba, tana cewa Sin na da ‘yancin daukar matakan da suka dace na kare halaltattun hakkoki da muradunta. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)













