Yayin da ake fara noman rani a sassan arewacin Nijeriya, manoma na nuna damuwa kan hauhawar farashin kayayyakin noma, rashin wadatattun kayan ban ruwa da kuma rashin samun lamuni mai saukin biya, wadanda suka ce suna ci gaba da kawo cikas ga kokarinsu na kara samar da abinci.
Duk da irin damar da noman rani ke da ita wajen karfafa noman damina da inganta samar da abinci, manoma da dama na kokarin ci gaba da ayyukansu sakamakon tsadar takin zamani, kayan ban ruwa da sauran muhimman kayayyakin noma.
Wasu manoma na ganin cewa magance wadannan matsaloli zai iya taimakawa wajen kara yawan amfanin gona, inganta samar da abinci da kuma taimakawa wajen rage farashin muhimman kayan abinci a kasar.
Sai dai sun jaddada cewa, idan ba a samar da isasshen tallafin gwamnati, samun kayan ban ruwa da kuma ingantattun matakan magance asarar amfanin gona bayan girbi ba, to damar da noman rani ke da ita wajen inganta wadatar abinci na iya ci gaba da kasancewa ba a yi amfani da ita yadda ya kamata ba.
Alhaji Nasiru Adamu Dabai, wani manomin tumatir daga Hunkuyi, cikin Karamar Hukumar Kudan ta Jihar Kaduna, ya ce manoma sun yi kokari da dama wajen neman tallafin gwamnati, amma har yanzu ba su samu wani gagarumin taimako ba.
A cewarsa, tsadar kayayyakin noma a kasuwa na ci gaba da sanya aikin noma cikin wahala, musamman ga kananan manoma wadanda suka fi dogaro da karancin kudaden da suke da su wajen gudanar da ayyukan noma.
Dabai ya bayyana cewa, manoma ba wai kawai suna fuskantar matsalar tsadar noman ba ne, har ma suna fuskantar manyan kalubale wajen adana amfanin gonarsu da sayar da shi bayan girbi.
Ya ce rashin isassun wuraren ajiya ya jefa manoma cikin asara mai yawa, musamman idan tumatir da sauran kayan lambu masu saurin lalacewa suka yi yawa a kasuwa a lokaci guda.
Manomin ya yi kira ga gwamnati da ta samar da ingantattun hanyoyin sayen amfanin gona a lokacin da kayayyakin suka yi yawa a kasuwa, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen kare manoma daga asara tare da karfafa musu gwiwa wajen fadada noman.
“Munn yin asarar miliyoyin naira a kowace shekara. Muna bukatar taimako,” in ji Nasiru
Ya jaddada cewa, tallafin gwamnati ga bangaren noma bai kamata ya tsaya kawai kan karfafa wa manoma gwiwa su kara samar da abinci ba, yana mai cewa akwai bukatar samar da hanyoyin da za su tabbatar da cewa ana adana amfanin gonar tare da sayar da shi cikin riba.
Haka kuma, Alhaji Mansur Aliyu Samaru, wanda gonarsa ta ke a kauyen Jaja, cikin Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna, ya bayyana damuwarsa kan cewa rashin magance matsalolin da manoma ke fuskanta na iya kawo cikas ga kokarin gwamnati na tabbatar da wadatar abinci.
Samaru ya ce noman rani na taka muhimmiyar rawa wajen karfafa noman damina, musamman wajen samar da abinci ga al’umma a lokacin da yawan amfanin gonar da ake samu ta hanyar noman damina ya ragu.
Ya bayyana cewa, manoman da ke gudanar da noman rani suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da samun kayan lambu da sauran kayayyakin noma a kasuwannin cikin gida.
Samaru ya yi gargadin cewa, yin watsi da wannan bangare na noma na iya haifar da mummunan sakamako ga wadatar abinci, yana mai jaddada cewa manoma na bukatar isasshen tallafi domin ci gaba da samar da abinci.
Ya yi kira ga gwamnati da ta ba da fifiko wajen bunkasa ban ruwa, samar da kayayyakin noma masu saukin farashi da kuma tallafin kudi ga manoma, yana mai cewa irin wadannan matakai za su taimaka wajen kara yawan amfanin gona da karfafa samar da abinci a kasar.














