Mai Faɗa Aji Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, ya buƙaci shugabannin ƙungiyar ‘PBAT Door-to-Door Movement’ da su yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Tompolo, wanda shi ne babban mai ɗaukar nauyin kungiyar, ya buƙaci ‘yan ƙungiyar da su bi lungu da sako dan ganin an wayar da kan al’umma zaɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu. Tompolo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake miƙa motoci guda 26 da kuma kaddamar da masu gudanar da kungiyar a jihar Gombe.
Haka kuma, masu gudanarwar sun karbi wasu kayan aikin yakin neman zabe daban-daban.Tompolo, wanda Babban Daraktan kamfanin Tantita Security Services Limited, Chief Kestin Pondi, ya wakilta, ya bukaci masu gudanarwar da su aiki tuƙuru dan ganin samun nasarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu.
A nasa jawabin, Gwamna Yahaya, wanda ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC za ta yi nasara a jihar Gombe tare da goyon bayan sake zaben Tinubu, ya ce manufofin shugaban kasar sun samar da damammaki don raya ababen more rayuwa da bunkasa fannin noma.













