Tashar CNBC (Consumer News and Business Channel) dake karkashin kafar NBC ta Amurka, a kwanan nan ta wallafa wata makala, inda take cewa, kamfanonin fasahar AI na kasar Sin suna ci gaba da rage tazarar aiki da ke tsakaninsu da manyan dakunan gwaje-gwaje na Amurka, har ma sun riga sun zarce su a wasu fannoni. A halin yanzu, mafi karfin aiki a duniya a cikin samfuran AI masu budadden tsari duk sun fito ne daga kasar Sin.
Ban da haka, masana da dama sun bayyana cewa, fasahar mutum-mutumin inji ta Sin ma tana kan kan gaba a duniya.
A cewar rahoton, samfuran fasahar AI na kasar Sin sun zama zabi mafi araha da inganci, kuma mai karfin takara idan aka kwatanta da na Amurka. Daniel Remler, wani babban jami’in bincike a shirin fasaha da tsaron kasa na cibiyar nazari ta CNAS (Center for a New American Security) ya bayyana cewa, bisa ga yadda al’amura ke gudana a halin yanzu, da alama damar da fasahar AI ta kasar Sin take da ita ta zama zabin farko ga kasashe masu tasowa na samun karuwar ci gaba.
Hakazalika, rahoton ya rawaito kalaman Keegan McBride, daraktan dake kula da manufofin fasaha na cibiyar nazari kan canjin duniya ta Tony Blair da ke kasar Burtaniya, wato TBI a takaice, yana cewa, a fannonin da za a kara yin amfani da fasahar AI da dama, ciki har da fasahar mutum-mutumin inji, da ta motoci marasa matuki, da kuma tafiyar da harkokin mulkin kasa, kasar Sin tana da fifiko a bayyane.” (Bilkisu Xin)














