Da safiyar yau Laraba, kasar Sin ta harba rokar Zhuque-3 da ake iya amfani da ita sau da dama, inda a karo na farko ta yi nasarar dawo da kasan rokar doron kasa. An harba rokar Zhuque-3 Y2 ce da misalin karfe 7:35 na safe agogon Beijing, daga cibiyar gwaji mai kula da harkokin sararin samaniya na kasuwanci ta Dongfeng da ke arewa maso yammacin kasar Sin.
An kammala dawo da kasan rokar doron kasa kamar yadda aka tsara, ba tare da ya ruguje ba, haka kuma an gudanar da aikin harba bangare mai tashi zuwa sararin samaniya cikin nasara.
Wannan ya biyo bayan nasarar da aka samu ta dawo da kasan rokar Long March-10B da aka yi a kan teku a ranar 10 ga watan Yuli.Bugu da kari, wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta yi nasarar dawo da kasan roka doron kasa ta hanyar amfani da kafafun sauka da ke jikinta, lamarin da ke nuna babban ci gaban da kasar ta samu a fasahar kera rokar da ake iya amfani da ita sau da dama. (Fa’iza Mustapha)














