Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, ya ce kasarsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen fadada bude kofarta ga ketare da inganta ci gaba mai inganci. Kuma katafariyar kasuwar kasar za ta samar da karin damammaki da zabi ga duniya.He Lifeng ya bayyana haka ne a jiya, lokacin da yake ganawa da Stephen Schwarzman, shugaban rukunin kamfanonin Blackstone a birnin Beijing.
A nasa bangare, Stephen Schwarzman ya ce kamfanin Blackstone na daukar hadin gwiwarsa da Sin da daraja, kuma a shirye yake ya fadada kasuwancinsa a kasar da bayar da gudummuwa wajen inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. (Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

Discussion about this post