ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dan Takarar ADC Ne Kadai Zai Raba Gardama A Zaben Shugaban Kasa Na 2027 —Kakakin Jam’iyyar

by Yusuf Shuaibu
5 months ago

Sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC, Malam Bolaji Abdullahi ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ne kadai zai raba gardama a zaben 2027, amma kuma jam’iyyar ce za ta iya yanke hukunci kan wa ye zai zama dan takara.

A yayin da yake magana kan jerin martanin da suka biyo bayan maganganun tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda shi ne sahu na  gaba wajen neman tikitin takarar jam’iyyar, cewa wannan yunkurin na yanzu zai kasance na karshe.

An fassara sharhin cewa Atiku yana nufin zai fafata takara da sauran ‘yan takarar shugaban kasa kamar Peter Obi, Rotimi Amaechi da Rabiu Musa Kwankwaso.

ADVERTISEMENT

Abdullahi ya ce jam’iyyar ita ce mafi girma kuma tana da iko na karsheakan yadda za ta fito da dan takararta na shugaban kasa.

Wasu goyon bayan ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC, sun riga sun fara jayayya kan wanda ya kamata ya dauki tutar takarar jam’iyyar a 2027.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Daya daga cikin shugabannin jam’iyya, Dele Momodu, ya ce tikitin Atiku/Obi zai kasance mafi kyau ga jam’iyya da Nijeriya.

Da yake jawaba a cikin shirin talabijin, shugaban kugiyar ‘Obedient Mobement’, Dakta Tanko Yunusa, ya jadaddada cewa mayar da tikitin takarar shuagaban kasa zuwa kudu shi ne kawai hanyar samun nasara a zaben da za su kori APC.

Ya ce tarbar girmamawa ga Obi da Kwankwaso daga wakilai a babban taron jam’iyyar na kasa ya nuna cewa suna da magoya baya masu dimbin yawa masu son su ga sun samu tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

“Lokacin da ya Obi zo jiharmu ta Kano, za a iya ganin hadin kai tsakaninsa da Rabiu Musa Kwankwaso. Tarbar ta kasance babba sosai, mun sha wuya kafin muka iya kula da taron jama’a. Ana ihu cewa sai Obi da Kwankwaso! Obi da Kwankwaso!” in ji shi.

Yayin da yake martani kan wannan lamari, Malam Abdullahi ya shaida cewa, “Masu goyon baya suna bayyana ra’ayinsu ne kawai, wanda abu ne na al’ada. Ba za su iya yanke hukunci ga jam’iyya ba. Suna bayyana ra’ayinsu da kuma burinsu ne kawai, wannan shi ne abin da suka yi.”

Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Tinubu Ya Gana da Gwamnan Kwara Bayan Harin Ta’addanci Da Ya Yi Ajalin Sama Da Mutane 160

Tinubu Ya Bayyana Dalilansa Na Yin Garanbawul A Majalisar Kasa

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.