Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a yau Talata cewa, kasar za ta tura sabbin jiragen sojin ruwa na rakiya zuwa mashigin tekun Aden da kuma yankunan ruwa da ke kusa da Somaliya a tsakiyar watan Agusta domin gudanar da aikin rakiya da tsaro.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta bayyana cewa, wannan shi ne karo na 49 da kasar Sin ke tura jiragen sojin ruwa na rakiya zuwa shiyyar, kuma an tsara hakan ne domin karbar ragamar aiki daga tawaga ta 48, wadda ta garzaya yankin a watan Oktoba na shekarar da ta gabata.
A bisa kudurorin Kwamitin Sulhun MDD da abin ya shafa, kasar Sin ta ci gaba da aika dakarun sojin ruwa masu rakiya a-kai-a-kai zuwa mashigin tekun Aden da yankunan ruwan tekun Somaliya tun daga shekarar 2008 domin kiyaye tsaron hanyoyin sufurin ruwa na kasa da kasa, inda ta yi wa jiragen ruwa na kasar Sin da na kasashen waje sama da 7,000 rakiya, gami da gudanar da ayyukan ceto, da ba da kariya, ko tallafa wa jiragen ruwan da ke neman dauki.
Kazalika, jiragen sojin ruwan sun kuma shiga aikin kwashe ’yan kasar Sin da na kasashen waje daga kasashen da yaki ya daidaita. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














