A wani mataki na kawo ƙarshen ƙaruwar rashin tsaro a Nijeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi gagarumin sauyi a shugabancin tsaro, ta hanyar bayar da umarnin ɗaukar sabbin ‘yan sanda da sojoji aiki, sannan ya janye ‘yan sanda daga tsaron manyan mutane.
Wannan sauyin ya haɗa da naɗin Janar Christopher Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro, wanda ya maye gurbin Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus daga muƙamin saboda dalilai na rashin lafiya.
- Tinubu Ba Zai Tattauna Da ’Yan Ta’adda Ba — Bwala
- Mutum 4 Sun Mutu Yayin Da ’Yan Bindiga Sake Kai Hari Kogi
Haka kuma, shugaban ƙasa ya sake naɗa sabbin shugabannin sojojin ƙasa, ruwa da sama.
Masana tsaro na ganin cewa wannan canjin shugabanci zai inganta haɗin gwiwar sojoji, dawo da ƙwarin gwiwar dakarun, da kawo sabbin dabaru a yaƙi da ‘yan ta’adda, ‘yan fashi da garkuwa da mutane, da sauran matsaloli da ke barazana da tsaro.
A lokaci guda, Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro a faɗin ƙasar na , inda ya ba da umarnin ɗaukar sabbin ‘yan sanda da sojoji aiki. Shirin ɗaukar ma’aikata ya tanadi ɗaukar sabbin jami’an tsaro, waɗanda za su samu horo a wurare daban-daban ciki har da sansanin horar da masu yi wa ƙasa hidima.
Manufar wannan mataki ita ce ƙara yawan jami’an tsaro domin kare yankunan da suka fi fuskantar barazana, musamman ƙauyuka da garuruwa da ke fama da hare-hare.
A wani mataki da ya jawo hankalin jama’a, shugaban ƙasa ya umarci janye ‘yan sanda daga aikin kare manyan mutane, inda za a mayar da su aikin kare al’umma.
A yanzu manyan mutane za su dogara ne wajen samun kariya daga hukumar civil defence da wasu hukumomi.
Wannan mataki na nufin dawo da dubban jami’an tsaro daga kare manyan mutane zuwa aikin da ya fi muhimmanci na kare rayuwar talakawa da al’umma gaba ɗaya.
Sauyin Zai Iya Kawo Tasiri – Bukarti
Masana tsaro kamar irin su Bulama Bukarti, sun bayyana cewa wannan sauyi zai iya kawo babban tasiri wajen rage rashin tsaro a faɗin Nijeriya, musamman a lokacin da barazanar garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda ke ƙaruwa.
“Mun sha kiran Gwamnatin Tarayya ta naɗa jakadu, ta kuma yi sauyi a fannin tsaro. Irin abin da shugaban ƙasa ya yi shi ne abin da ake tsammani tuntuni,” in ji Bukart.
Gwamnatin ta kuma ɗauki mataki na ƙarfafa dangantakar diplomasiyyar Nijeriya, inda Shugaba Tinubu ya aike sunayen mutane da Majalisar Dattawa za ta tantance a matsayin waɗanda zai yi muƙamin jakadu.
Wannan mataki na da nufin dawo da Nijeriya cikin sahun ƙasashen da ke da ƙarfin dangantaka da ƙasashen waje, wajen samun bayanai kan tsaro, haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci, da samun tallafi na ƙasashen waje, wajen horarwa da kayan aiki.
Masanan sun ce ƙarfafa dangantaka da ƙasashen waje na iya taimakawa wajen daƙile ayyukan ‘yan ta’adda da garkuwa da mutane da kuma sauran laifuka.
Wannan Lokaci Ne Mai Matuƙar Muhimmanci – Masani
Sai dai, masana tsaro sun yi gargaɗin cewa nasarar wannan shiri za ta dogara ne a kan: horarwa mai inganci, samun kuɗaɗen masu ɗorewa, gaskiya, da kuma magance tushen rashin tsaro kamar talauci, rashin aikin yi, rashin ingantaccen shugabanci da kuma rashin haɗin kai a tsakanin hukumomi.
“Wannan lokaci ne mai matuƙar muhimmanci,” in ji Dr. Musa Abubakar, ƙwararre a fannin harkar tsaro a Abuja.
“Ƙalubale yanzu shi ne tabbatar da manufofi a aikace, ganin cewa ‘yan sanda da aka mayar bakin aiki, da kowane aiki na soja ya kawo bambanci ga rayuwar ‘yan Nijeriya.”
Hakazalika, matakin zai iya kawo sauki a wuraren da aka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane, inda sabbin jami’an tsaro za su ƙara yawan tsaro a ƙauyuka da garuruwa, da kuma rage hargitsi a manyan tituna.
Matakin Na Iya Zama Juyin Juya Hali
Masu sharhi kan harkokin tsaro sun bayyana cewa, wannan mataki na Tinubu na iya zama juyin juya hali ga tsarin tsaro a Nijeriya, musamman idan aka aiwatar da shi yadda ya kamata.
Yayin da Najeriya ke kallon wannan mataki, matakan gwamnatin Tinubu na iya zama wani juyin juya hali a yaƙi da matsalar tsaro ko kuma su kasance wani babban sauyi mai ɗaukar hankali ba tare da tasiri mai ɗorewa ba.
Amma idan aka aiwatar da wannan shiri da gaskiya, horo mai inganci, da kyakkyawan tsarin aiki, akwai yiwuwar Nijeriya za ta ga ingantaccen tsaro a cikin watanni masu zuwa, wanda zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a faɗin ƙasar nan.














