ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Ɗage Shari’ar El-Rufai Kan Zargin Almundahana Da Kuɗaɗe Zuwa 30 Ga Nuwamba

by Sadiq
2 weeks ago

Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ɗage ci gaba da shari’ar tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, kan zargin almundahana da kuɗaɗe zuwa ranakun 30 ga watan Nuwamba da 1 ga watan Disamban 2026.

An ɗage shari’ar ne a ranar Talata domin ci gaba da yi wa ƙwararren jami’in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) kan binciken na’urorin sadarwa, Shegun Kayode, tambayoyi a kotu.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Darius Khobo, ya yi watsi da ƙin amincewa da shaidar da lauyoyin El-Rufai suka yi, inda ya ba da damar ci gaba da sauraron shaidar ƙwararren duk da cewa ba a saka sunansa cikin jerin shaidun masu gabatar da ƙara ba.

ADVERTISEMENT

Kayode ya shaida wa kotun cewa DSS ta binciki wasu sautin murya da bayanan sadarwa da ake zargin suna da alaƙa da El-Rufai da wasu abokansa, bisa buƙatar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC).

Ya yi zargin cewa sautin muryar ya ƙunshi tattaunawa kan shirye-shiryen kawo cikas ga binciken da Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ke gudanarwa, da kuma zargin ware dala 500,000 da dala 100,000 domin biyan jami’an da ke bincike.

LABARAI MASU NASABA

ADC Ta Yi Wa APC Ba’a Kan Zargin Hayar Taron Jama’a Da Rashin Cika Kujeru A Taron Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

Sai dai har yanzu kotu ba ta tabbatar da waɗannan zarge-zarge ba.

ICPC na tuhumar El-Rufai da laifuka tara da suka haɗa da zargin cin hanci da rashawa da amfani da muƙami ba bisa ƙa’ida ba a lokacin da yake mulkin Kaduna.

Zarge-zargen sun haɗa da almundahana da kuɗaɗen gwamnati, bayar da kwangilar CCTV ba bisa ƙa’ida ba da kuma almundahana da kuɗin rancen Bankin Duniya.

El-Rufai ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa.

Kotun za ta ci gaba da sauraron shari’ar a ranakun 30 ga watan Nuwamba da 1 ga watan Disamba domin ci gaba da binciken shaidar jami’in DSS.

MASU ALAKA

Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo
Siyasa

ADC Ta Yi Wa APC Ba’a Kan Zargin Hayar Taron Jama’a Da Rashin Cika Kujeru A Taron Kaduna

October 25, 2026
An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna
Manyan Labarai

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai
Manyan Labarai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Next Post
2027: An Shirya Wa Matasa Bita Kan Guje Wa Kalaman Kiyayya A Kaduna

2027: An Shirya Wa Matasa Bita Kan Guje Wa Kalaman Kiyayya A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Tura Dakarunta Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Yankin Olle-Bunu Na Jihar Kogi

Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 15 Ta Harin Sama A Borno

October 25, 2026
2027: Hana Tinubu Wa’adi Na Biyu Na Iya Jefa Nijeriya Cikin Rikicin Siyasa — Pakistan

Tinubu Ya Cancanci A Sake Zaɓensa A 2027 — Pakistan

October 25, 2026
Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jihar Taraba Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 40

Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jihar Taraba Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 40

October 25, 2026
Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo

ADC Ta Yi Wa APC Ba’a Kan Zargin Hayar Taron Jama’a Da Rashin Cika Kujeru A Taron Kaduna

October 25, 2026
An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.