ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Yanke Wa Tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman Hukuncin Shekaru 75 A Gidan Yari

by Sulaiman
4 months ago
Mamman

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75 a gidan yari bayan samun sa da laifin karkatarwa da halasta kuɗaɗen da aka ware domin aikin wutar lantarkida suka kai naira biliyan 33.8.

An same Mamman da laifi a dukkan tuhume-tuhume 12 da Hukumar EFCC ta shigar a kansa.Mai shari’a James Omotosho ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a kan tuhume-tuhume 10, yayin da aka yanke masa shekaru uku da shekaru biyu a tuhume-tuhume na huɗu da na biyar bi da bi.

Kotun ta ce za a aiwatar da hukuncin ɗaya bayan ɗaya ba tare da zaɓin biyan tara ba, sai dai tuhume-tuhume na huɗu wanda aka ba da damar biyan tarar naira miliyan 10.

ADVERTISEMENT

Mai shari’ar ya kuma bayar da umarnin ƙwace kuɗaɗen ƙasashen waje da aka samu daga hannun wanda aka yankewa hukunci, tare da wasu manyan kadarori huɗu masu tsada da ke Abuja da aka danganta su da shi.EFCC ta gurfanar da Mamman a watan Yulin 2024 kan zargin halasta kuɗaɗen haram da haɗa baki da wasu jami’an Ma’aikatar Wutar Lantarki da kamfanoni masu zaman kansu wajen karkatar da kuɗaɗen ayyukan samar da wutar lantarki na Zungeru da Mambilla.

Mamman ya musanta dukkan zarge-zargen da ke cikin shari’a mai lamba FHC/ABJ/CR/273/2024.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

A yayin shari’ar, EFCC ta gabatar da shaidu 17 tare da gabatar da hujjoji 43 kafin ta rufe shari’arta.

A ranar 7 ga Mayu, kotun ta same shi da laifi, inda yaki kasancewa a kotu, inda Mai shari’a Omotosho ya ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da zargin ba tare da wata shakka ba.

Daga nan ne kotun ta bayar da sammacin kama shi bayan lauyansa, Mohammed Ahmed, ya bayyana cewa bai san inda wanda yake karewa yake ba kuma duk ƙoƙarin samun sa ta waya ya ci tura.

Bayan yanke hukuncin, alkalin ya umarci hukumomin tsaro su yi haɗin gwiwa da jami’an tsaro na kasa da kasa domin tabbatar da kamo Mamman.

Kotun ta kuma bayyana cewa wa’adin zaman gidan yarin zai fara ne daga ranar da aka kama shi.

Mamman
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Surikar Sarki Aminu Ado Bayero Ta Rasu

Surikar Sarki Aminu Ado Bayero Ta Rasu

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.