Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Kaduna ta ajiye hukunci kan ƙarar tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke ƙalubalantar ƙin amincewa da bukatarsa ta beli da Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yi.
Lauyan ICPC, Ayodeji Adedipe, ya roƙi kotun da ta yi watsi da ƙarar, yana cewa El-Rufai ya gabatar da bukatar beli sau uku a ƙaramar kotu, amma duk an ƙi amincewa da su.
Sai dai lauyan El-Rufai, Paul Erokoro, SAN, ya nemi Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta soke hukuncin ƙaramar kotun tare da bayar da belin wanda yake karewa. Ya ce laifukan da ake tuhumar tsohon gwamnan da su ba na kisa ba ne, don haka babu hujjar hana shi beli.
Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Onyekachi Aja Otisi, ta saurari ɓangarorin biyu kafin ta ajiye hukunci zuwa wata rana da ba a bayyana ba.














