ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotun Abuja Ta Hana INEC Amincewa Da Tarukan ADC

by Sulaiman
5 months ago
inec

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta hana Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) amincewa ko halartar duk wani taron jam’iyyar ADC da wasu wakilan shugabancin riƙon ƙwarya na ADC ya shirya.

A hukuncin da Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta yanke ranar Laraba, kotun ta kuma hana tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, da wasu jiga-jigan jam’iyyar tsoma baki cikin ayyukan shugabannin jihohi da aka zaɓa wanda wa’adinsu bai ƙare ba.

Hukuncin ya kawo wani sabon salo a rikicin shugabanci da ya daɗe yana addabar ADC, wanda zai iya yin tasiri kan ikon tafiyar da tsarin jam’iyyar kafin manyan harkokin siyasa masu zuwa.

ADVERTISEMENT

Wasu mutane bakwai ƙarƙashin jagorancin Norman Obinna ne suka shigar da ƙarar a madadin shugabannin jihohi da kwamitocin gudanarwa na ADC a faɗin ƙasar.

Sun ƙalubalanci halaccin matakan da shugabancin riƙon ƙwarya na ƙasa ya ɗauka, musamman yunkurin shirya tarukan jihohi ta hannun wani kwamiti da aka naɗa.

LABARAI MASU NASABA

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

Masu ƙarar sun kafa hujjar cewa shugabancin riƙon ƙwaryar ba shi da hurumin kundin tsarin mulkin jam’iyyar na shirya taruka ko kafa kwamitoci domin hakan, suna masu cewa hukumomin da aka zaɓa bisa tsarin jam’iyyar ne kawai ke da ikon gudanar da irin waɗannan ayyuka.

Sun roƙi kotun da ta tabbatar da wa’adin shugabannin jihohin da ke kan mulki tare da hana duk wani tsarin da zai iya raunana ikonsu.

ADC
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
  • Sulaiman
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • Sulaiman
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • Sulaiman
    Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

MASU ALAKA

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
Labarai

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026
Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
Labarai

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC
Labarai

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Next Post
An Mika Ginin Helkwatar ECOWAS Wanda Sin Ta Tallafa Wajen Ginawa Ga Kungiyar

Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.