Kotun koli ta tabbatar da zaben Dauda Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin Gwamnan Jihar Zamfara.Â
Kotun koli ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, wadda ta bayyana zaben gwamnan jihar a matsayin wanda bai kammala ba.
- Kotun Koli Ta Tabbatar Da Abba Kabir Yusuf A Matsayin Zababben Gwamnan Kano
- Shari’ar Kano: Gwamna Yusuf Da Mataimakinsa Sun Halarci Zaman Kotun Koli
Dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar, Bello Matawalle na rike da mukamin karamin ministan tsaro.
Matawalle ya zargi INEC da yin watsi da nasarar da ya samu a zaben ta hanyar kasa hada sakamakon wasu yankunan a jihar.
Kotun kolin ta yi watsi da karar Matawalle tare da tabbatar da Dauda Lawal a matsayin halastaccen Gwamnan jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp