Jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna ta bayyana cewa rashin mulki ke sanya Dan takarar shugaban kasa na jamiyyar ADC Alhaji Atiku Abubakar yin furuci kara zube.
Ya bayyana cewa firgici da kuma rashin samun damar mulki ne suka sanya tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yin kalaman suka ga gwamnatin APC mai ci.
Kakakin jam’iyyar na jihar Kaduna, Mohammed Sani Haruna, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a sakatariyar APC da ke Kaduna.
Mohammed Sani ya jaddada cewa jam’iyyar APC ba ta shakkar ko wace irin jam’iyyar adawa, duba da irin kyakkyawan shugabanci da aka gina shi kan ayyukan raya kasa.
Ya ci gaba da cewa, jam’iyyar ta riga ta kammala duk wani shiri na fitar da dabarun tallata shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani.
Kakakin ya Kara da cewa a duk tarihin jihar Kaduna ba a taba samun gwamna da ya kawo ci gaba a birni da karkara kamar Gwamna Uba Sani ba.
Don haka, Mohammed Sani ya bukaci daukacin al’umma da su cigaba da bai wa gwamnatin APC goyon baya duk da cewa akwai ’yan matsalolin da ba za’a rasa ba, yana mai tabbatar da cewa gwamnati tana tsaye wajen cika alkawuran da ta dauka.














