Kungiyar masana’antun auduga ta Sin ko CCA, ta yi matukar kalubalantar matakin Amurka na sanya karin kamfanonin kasar Sin 43, ciki har da kamfanonin sarrafa auduga, cikin jadawalin da ta kira na “Dokar dakile kwadagon tilas na ‘yan Uyghur”, tana mai bayyana hakan a matsayin tsantsar keta dokokin cinikayya na kasa da kasa.
Wata sanarwa da kungiyar ta CCA ta fitar a ranar Asabar, ta ce zargin da Amurka ta yi game da “kwadagon tilas” ba shi da tushe ko goyon bayan doka, kuma masana’antun auduga na Sin na bin tsarin kasuwa da salon neman ci gaba na zamani.
Sanarwar ta kara da cewa, a jihar Xinjiang, yankin da shi ne kan gaba wajen sarrafa auduga, a yanzu ana gudanar da sama da kaso 90 bisa dari na girbin auduga ta amfani da na’urori, kana ana gudanar da akasarin ayyuka da injuna masu sarrafa kansu, tun daga shuka har zuwa girbi da sarrafa kayayyakin auduga.
A daya bangaren kuma, ana matukar martaba hakkoki da moriyar manoman auduga, da ‘yan kwadago karkashin dokokin kasar Sin, yayin da kuma ma’aikata ke gudanar da ayyuka bisa radin kan su, wato dai babu wani batu na tilasawa ma’aikata yin kwadago ala tilas.
Daga nan sai kungiyar ta zargi gwamnatin Amurka da yin watsi da gaskiya, tare da shafawa kamfanonin kasar Sin kashin kaji, tana mai cewa manufar Amurka ita ce siyasantarwa, da mayar da batutuwan kare hakkin bil’adama makami, na yakar ci gaban sashen samar da auduga da masakun kasar Sin. (Saminu Alhassan)













