ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Li Qiang Ya Gana Da Shugabannin Bankin Duniya Da IMF Da MDD

by Sulaiman
7 months ago
Li Qiang

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana a jiya Talata da shugaban bankin duniya Ajay Banga da darektar asusun ba da lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva da sakatariyar MDD mai kula da harkokin ciniki da ci gaba Rebeca Grynspan, wadanda ke halartar taron koli na tattaunawa kan tattalin arzikin kasa da kasa tsakanin Sin da kungiyoyin tattalin arziki 10 na duniya da ake kira “1+10.”

Li Qiang ya bayyana cewa, tattalin arzikin Sin na ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da tangarda ba, kuma yana ci gaba da ba da karfinsa wajen samar da tabbaci da kwanciyar hankali ga tattalin arzikin duniya. Ya ce a cikin shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15, tattalin arzikin Sin zai ci gaba da inganta. Yana mai cewa, Sin tana ci gaba da bude manyan kasuwanninta ga duniya, kuma tana gabatar da damammakin ci gaba tare da mabambantan kasashe, kuma za ta warware rikice-rikicen ciniki ta hanyar karfafa tattaunawa, ta yadda za a kara inganta moriyar juna.

Li Qiang ya kara da cewa, Sin na goyon bayan tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD, kuma tana tallafawa ayyukan kungiyoyin raya tattalin arziki na kasa da kasa. Haka kuma tana son taimakawa mabambantan bangarori su bi ingantaccen tsarin kasa da kasa na gaskiya, da inganta daidaiton tsarin cudanyar mabambantan bangarori a duniya, da kuma ci gaban tattalin arzikin duniya mai gamsar da kowa.

ADVERTISEMENT

A nasu bangare, Ajay Banga, Kristalina Georgieva, da Rebeca Grynspan sun ce, shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15 zai baiwa tattalin arzikin duniya tabbaci da karfi masu inganci. Bangarori daban-daban na fatan ci gaba da bin tsarin kasa da kasa tare da Sin, don kiyaye tsarin cudanyar mabambantan bangarori a duniya da iko da kimar MDD, da kuma inganta tsarin jagorantar harkokin duniya. (Amina Xu)

LABARAI MASU NASABA

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

Li Qiang
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka
  • Sulaiman
    Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi
  • Sulaiman
    CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai
  • Sulaiman
    Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

MASU ALAKA

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai
Daga Birnin Sin

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026
Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma
Daga Birnin Sin

Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

July 14, 2026
Next Post
Pogba Ya Zuba Hannun Jari A Wasan Tseren Raƙumi A Ƙasar Saudiyya

Pogba Ya Zuba Hannun Jari A Wasan Tseren Raƙumi A Ƙasar Saudiyya

LABARAI MASU NASABA

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026
Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026
ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

July 14, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato

Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP A Borno

July 14, 2026
Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

July 14, 2026
Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

July 14, 2026
“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

July 14, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.