Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jinjina wa gwamnatin Ƙasar Saudiyya da gidauniyar tallafi ta Sarki Salman (King Salman Humanitarian Aid and Relief Centre) kan gudanar da aikin tiyatar mafitsara da cututtukan da suka shafi fitsari (urological surgeries) kyauta ga marasa lafiya 52 a jihar.
Aikin tiyatar, wanda ƙungiyar ƙwararrun likitoci daga Saudiyya ta gudanar a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) na tsawon kwanaki shida, ya mayar da hankali ne wajen tallafa wa gajiyayyu da marasa ƙarfi waɗanda ba su da ikon biyan kuɗin irin waɗannan manyan ayyukan lafiya. Jagoran tawagar likitocin, Dr. Ali Ibn Mahfouz, ya tabbatar da cewa an yi dukkan tiyatar cikin nasara ba tare da samun wata tangarɗa ko matsala ba.
Da yake jawabi a wurin bikin rufe shirin a ranar Juma’a, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa wannan shi ne karo na huɗu da tawagar likitocin Saudiyya ke kawo irin wannan ɗauki a Kano, inda ya tuna da aikin tiyatar ido kyauta da aka yi wa mutane sama da 2,300 a shekarar 2023, da kuma aikin raba ƴan biyun da aka yi a Saudiyya.
Haka kuma, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙarfafa alaƙa da ƙasar Saudiyya a fannin kiwon lafiya, yana mai sanar da cewa an riga an fara shirye-shiryen fara gudanar da aikin tiyatar zuciya (open-heart surgery) kyauta a Kano. Ya kuma miƙa godiyarsa ga shugabancin asibitin AKTH da Ofishin Jakadancin Saudiyya a Nijeriya ƙarƙashin Babban Jami’in Ofishin a Kano, Sheikh Khalil Ahmad.
A ƙarshe, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da inganta asibitoci, da ɗaukar sabbin ma’aikatan lafiya aiki, da kuma faɗaɗa hanyoyin samar da ingantacciyar kulawar lafiya ga al’ummar Jihar Kano.














