Ma’aikatan gwamnati ƙarƙashin Majalisar Ƙasa ta Haɗin Kan Kungiyoyin Ma’aikatan Gwamnati (JNPSNC) sun yi barazanar fara yajin aikin gargadi na ƙasa baki ɗaya daga ranar 2 ga Oktoba, matuƙar Gwamnatin Tarayya ta gaza mayar da martani ga buƙatunsu.
Majalisar ta ce za ta fara yajin aikin ne idan gwamnati ba ta ɗauki matakan da ake buƙata ba a cikin wa’adin da ta bayar, ciki har da rage farashin man fetur.
Ƙungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ita ma ta bayyana goyon bayanta ga barazanar da ma’aikatan gwamnati suka yi.
A ranar 30 ga Satumba, 2026, ma’aikatan sun bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adi kan tashin farashin man fetur, buƙatar a ba ma’aikata ƙarin alawus na musamman (wage award) da kuma fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.
JNPSNC, wadda ta ƙunshi ƙungiyoyin ma’aikata takwas a ɓangaren gwamnati, ta ce za ta gudanar da yajin aikin gargadi na kwanaki uku idan gwamnati ta gaza rage farashin man fetur zuwa ₦500 kan lita, ta sanar da ƙarin alawus ga ma’aikata, tare da ɗaukar wasu matakan rage wa jama’a radadin matsin tattalin arziki.
Ƙungiyoyin da ke cikin JNPSNC sun haɗa da NCSU, M&HWU, ASCSN da NANNM).
Sauran su ne AUPCTRE, NUPSRAW, NUPPPPROW, da NUAEE.
Majalisar ta ce ta shirya tare da tattara ma’aikatan gwamnati a faɗin ƙasar domin shiga yajin aikin gargadi, idan Gwamnatin Tarayya ta gaza magance matsalolin da aka gabatar wa Shugaba Bola Tinubu kafin cikar wa’adin.














