Reshen jam’iyyar ADC na Jihar Borno ya yi kakkausar suka kan kama matasa biyar da jami’an tsaro suka yi bisa zargin sanya riga mai ɗauke da tambarin “Tinubu Must Go” a Maiduguri, babban birnin jihar.
Jam’iyyar ta bayyana kamen a matsayin kamun da ya saɓa wa doka, tana mai cewa matasan ba su aikata wani laifi ba ta hanyar bayyana ra’ayinsu na siyasa.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ADC a jihar, Hon. Baba Ahmed Mustapha, ya sanya wa hannu a daren Talata.
Ya ce jam’iyyar ta samu labarin kamawa da tsare matasan biyar cikin mamaki da damuwa, yana zargin cewa jami’an tsaro sun aiwatar da kamen ne bisa umarnin jam’iyyar da ke mulki, saboda matasan sun sanya riga mai ɗauke da tambarin “Tinubu Must Go.”
Ya ce ADC na yin Allah-wadai da abin da ya bayyana a matsayin “mataki na rashin bin tsarin dimokuraɗiyya, wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulki kuma mai tayar da hankali.”














