Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta kammala cinikin dan kwallon tawagar Uruguay, Darwin Nunez daga kungiyar kwallon kafa ta Benfica dake kasar Portuga kan yarjejeniyar kakar wasa shida kuma kan fam miliyan 64.
Nunez mai shekara 22 a duniya zai zama dan wasa mafi tsada da kungiyar ta saya a tarihi, idan aka hada da kudin tsarabe-tsarabe da zai kai fam miliyan 85 jumulla kuma dan wasan ya ci kwallo 34 a wasanni 41 da ya yi wa Benfica a kakar da aka kammala.
Wanda Liverpool ta dauka da kudi da yawa a tarihi, shi ne dan wasan baya Birgil ban Dijk, kan fam miliyan 75 daga Southampton a 2018, kuma kudin da aka sayo Nunez zai karu zuwa fam miliyan 85, idan har zai ke buga wasa a koda yaushe.
Kudin karin tsarabe-tsaraben ya kunshi kwallo nawa zai ci da idan Liverpool ta dauki Champions League da kuma gasar firimiyar Ingila a kakar wasa guda daya wanda kungiyar taso yi a wannan kakar.
Nunez, wanda ya ci wa Uruguay kwallo 11, ya zura kwallaye 26 a raga a karawa 28 a babbar gasar kasar Portugal a kakar wasa ta shekara ta 2021 zuwa 2022 – guda 25 da ya ci da shi aka fara wasa.
Ya kuma ci kwallaye shida a wasanni 10 a kofin zakarun turai na Champions League da aka karkare, har da wadanda ya zura a ragar Liverpool a karawa gida da waje a zagayen wasan kusa da na kusa da na karshe cikin watan Afirilu.
Liverpool ta lashe Carabao Cup da FA Cup a kakar da ta kare ta kuma yi ta biyu a Champions League, bayan da Real Madrid ta dauki na 14 jumulla duk da cewa kociyan kungiyar ya bayyana cewa za su samu damar komawa a kakar wasa ta gaba.