ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wacce Kasa Ce Za Ta Lashe Gasar Kofin Afirka

by Abba Ibrahim Wada
9 months ago
Kofin

Gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2025, wadda aka shirya gudanarwa a Morocco daga ranar 21 ga watan Disamba, 2025 zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2026, tana daga cikin gasannin da ba a iya hasashen kasar da za ta lashe ba a tarihin gasar.

Kuma tun da aka fara buga gasar a shekarar 1957 ba a taba samun gasar da ake hasashen kasashe biyar ko shida na iya lashewa ba kamar ta bana saboda yadda kasashe da dama suke da manyan ‘yan wasa. Baya ga Morocco mai masaukin baki, akwai wasu kasashe da dama da ake ganin suna kan gaba cikin jerin wadanda ka iya nasara, wato Senegal da Masar da Ibory Coast da kuma Aljeriya, wadanda tuni suka samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026.

  • Za A Fara Gasar Wasanni Ta Nakasassu Da Masu Bukata Ta Musamman Ta Sin
  • Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimaka Wa Kasashen Yankin Tsakiyar Afrika Karfafa Tsaronsu

Daya daga cikin abubuwan al’ajabi a gasar cin kofin nahiyar Afirka shi ne yadda ba a iya samun tabbacin kasar da za ta lashe ta. A karo na takwas na baya-bayan nan dai an samu zakaru bakwai daban-daban, inda Ibory Coast ce kadai ta samu kambu sau biyu daga cikin gasa biyar da suka gabata, a 2015 da 2024.

ADVERTISEMENT

Karkashin jagorancin mai koyarwa Walid Regragui, Morocco, kasar da ke kan gaba a jerin kasashen Afirka a jadawalin FIFA, ta taka rawar gani a fagen kwallon kafa a duniya a shekarar 2022, inda ta zama tawagar Afirka ta farko da ta buga wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya.

Ba kasancewa a gida ba ne kadai abin da ke kara wa tawagar kasar Morocoo kwarin gwiwa ba a gasar bana, amma tawagar na da babban buri na tabbatar da lashe gasar cin kofin kasashen Afirka karo na biyu tun shekarar 1976.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

A gaban al’ummar kasarta, tawagar Morocco na da burin samun makoma irin ta Ibory Coast, wato nasara a gida amma ba tare da fargabar da ta fuskanta a zagayen farko ba.

Amma karbar bakuncin gasar ba lallai ba ne ya zame riba ba. A cikin karo 34 da aka gudanar da gasar tun daga shekarar 1957 (ciki har da gasar farko), sau 12 ne kacal kasar da ta karbi bakuncin gasar ta yi nasara, wato kusan kashi 35% cikin dari. Tun daga 2000, Tunisia (2004), da Masar (2006) da Ibory Coast (2024) ne kawai suka yi nasara a gida.

Kasar da ta fi fice a Afirka na da burin lashe kambu na takwas don kawar da bakin cikin kashin da ta sha a hannun Senegal a wasan karshen gasar 2022. ‘Yan wasan tawagar Masar na da ta hadin matasa da kuma gogaggu. Wannan garwayen ‘yan wasan na ba ta damar taka muhimmiyar rawa a wasannin nahiyoyi a kusan kodayaushe. Karkashin jagorancin Hossam Hassan, Masar tana wasa da sauri, yayin da ta ci gaba da amfani da dabarun wasa da aka san ta da su.

Omar Marmoush da Mostafa Mohamed su ne misalan ‘sabbin jini’ a tawagar, yayin da suke daukar darasi daga tauraron tawagar Mohamed Salah wanda ake hasashen zai taka muhimmiyar rawa a gasar bana a Morocco.

Bayan da ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka a gida a shekarar 2024, tawagar Elepahants ta shiga gasar bana a matsayin mai rike da kambun gasar. Nan da nan wannan ya sanya ta zama cikin jerin wadanda ake kyautatawa zaton lashe gasar, wadda ta taba lashewa sau uku, ciki har da sau biyu a gasanni biyar na baya bayan nan.

A karkashin jagorancin Emerse Faé, tawagar Elephants ta isa Morocco da burin ci gaba da rike kambunta. Amma akwai alamun za ta fuskanci kalubale da dama daga wasu kasashen.

Tun lokacin da aka fara gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) a shekarar 1957, kasashe uku ne kawai suka iya kare kambunsu. Masar ta yi haka a shekarar 1957 da 1959, sannan kuma ta sake yi a 2006, 2008, da 2010. Ghana ta yi nasara a 1963 da 1965, Kamaru a 2000 da 2002.

Senegal, wadda ta lashe kambunta na farko shekara hudu da suka gabata bayan dogon jira da kuma rashin nasara biyu a matakin wasan karshe (2002 da 2019), ta kasance ‘yar takarar da za ta taka muhimmiyar rawa a gasar.

Bayan lashe gasar AFCON 2021, amma an fidda ta da wuri shekara biyu bayan haka, da alama ta fara samun daidaito a karkashin jagorancin Pape Thiaw, wanda ya gaji Aliou Cissé.

Yayin da tawagar ke dauke gogaggun ‘yan wasa kamar Sadio Mane da Kalidou Koulibaly da Idrissa Gueye, Lions na Teranga za su iya yin la’akari da cewa ta na da matasan ‘yan wasa masu hazaka da ke da gogewar yin nisa na gasar nahiyar.

Tawagar Senegal, da ta Morocco, su ne manyan tawagogin Afirka biyu a saman jadawalin FIFA, a matsayi na 18 da 12 bi da bi. Senegal, wadda ta mamaye rukuninta na neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026, za ta dogara kan ci gaban da ta ke samu ta fannin ‘yan wasa da don maimaita nasarar da ta samu a 2022.

Bayan rashin nasara sau biyu a gasar AFCON na 2021 da 2023 inda aka fitar da ita a matakin rukuni, tawagar Fennecs na son bude wani sabon babi a tarihinta na gasar. Bayan zamanin Belmadi, inda ta yi farin cikin nasara a 2019 sannan kuma ta yi rashin nasara biyu (CAN 2021 da Gasar Cin Kofin Duniya 2022), Algeria ta tunkari CAN 2025 da babban burin: sake kasancewa tawagar kwallon kafa da ke kololuwar wasa a nahiyar.

Domin cimma wannan burin, hukumar kwallon kafar kasar ta dogara ga koci Bladimir Petkobić, da kasar Serbia wanda ya yi suna bayan da ya horas da tawagar Switzerland da ta yi gogayya da manyan kasashen Turai. ‘Yan wasan da suka lashe gasar cin kofin Afrika a 2019 sannu a hankali sun dusashwewa, suna ba da dama ga sabbin matasan ‘yan wasa da suka hada da Fares Chaïbi da Houssem Aouar da Rayan Aït Nouri, da Badredine Bouanani.

Aljeriya ta kasance babbar abokiyar hamayya ga tawagogin ‘yan wasan nahiyar da dama, wadda za ta iya tabuka abin kirki a kowace gasa. Idan Petkobic ya sami nasarar daidaita tawagarsa, Fennecs na iya sake zama kamar tawagar da ta mamaye fagen wasan kwallon kafan Afirka a 2019.

 

Ko Nijeriya Za Ta Iya Taka Rawar Gani?

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta tsinci kanta a rukunnin C a gasar bana inda za ta fafata da Tunisia da Uganda da kuma Tanzania. Super Eagles dai za ta nemi kawar da bakin cikin da ta fuskanta a wasan karshen gasar da ta gabata inda ta yi rashin nasara a hannun Ibory Coast a wasan karshe duk da cewa ita ta fara jefa kwallo a raga a wasan.

Nijeriya wadda ta ke da kambun AFCON guda uku, a shekarun 1980, 1994, da 2013, wanda hakan ya sanya ta zama daya daga cikin kasashen da suka fi samun nasara a gasar ta Afirka.

Kasancewa tana da manyan ‘yan wasa kamar su Bictor Osimhen da Ademola Lookman da ke buga wasa a manyan kungiyoyin kasashen Turai ana ganin cewa kasar za ta iya tabuka abin a zo a gani a gasar bana, duk da cewa dai rashin nasarar da ta yi a yunkurinta na samun gurbi a gasar cin kofin duniya na 2026 na sanya alamar tambaya kan rawar da za ta iya takawa.

Kociyan tawagar ta Nijeriya, Eric Chelle, na shirin kara inganta tawagar tasa da wasu sabbin ‘yan wasa guda hudu ko biyar domin tabbatar da cewa Super Eagles din ta kai bantanta a Moroko.

Wasu daga cikin sababbin ‘yan wasan da za a iya kira shi ne dan wasan baya na Blackburn Robers Ryan Alebiosu, wanda tsohon dan wasan bangaren matasa na Arsenal ne kuma a halin yanzu yana taka rawar gani a gasar Championship ta Ingila. Wani sabon dan wasan da aka sanya wa ido shi ne dan wasan tsakiya Ebenezer Akinsanmiro da ke zaman aro a kungiyar Pisa daga Inter a gasar Serie A ta Italiya.

Rauni zai hana dan wasan Nottingham Forest Ola Aina buga gasar, yayin da Bright Osayi-Samuel ke fama da rashin tagomashi a kungiyarsa ta Birmingham City ta Ingila.

Amma duk da haka ba za a iya cire rai cewa Super Eagles za ta taka rawar gani a gasar ba, saboda dimbin tarihin da ta ke da ita a gasar, kuma ana ganin ‘yan wasan za su zo da niyyar huce fushin rashin samun gurbi a gasar cin kofin duniya ta 2026.

Kofin
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
Kofin

Samarwa Sojoji Manyan Makamai Ne Mafita - Shugaban Ƙaramar Hukumar Bukuyum

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.